ukarofi

12664 Posts
Mafitar Arewa

Mafitar Arewa

Duk wanda ya ke kallon cakuɗewar lamura a arewa zai san samun mafita tafiya ce mai tsawo. Dalilai na su ne, ga maciji amma ana nuna igiya, wato yadda duk wani laifi ƙarami ko babba kowa ke kallon kamar sai shugaban ƙasa ko gwamnan jiha ke iya magance shi. Misali wani abun takaici za ka ji mutum ya fito a kafafe na sadarwa yana faɗin matsaloli wanda abokan zamanmu na kudanci ba haka su ke yi ba. Kuma mu kula hatta a cinikayya a tsakanin shaguna na unguwa da ababe da ba a kai su shago kamar kayan gwari duka…
Read More
Mu guji yaɗa labaran ƙarya a yanar gizo

Mu guji yaɗa labaran ƙarya a yanar gizo

Fatan alheri ga Manhaja, yau wasiƙata za ta mayar da hankali ne kan ’yan jaridar Intanet, masu rubutun wallafa labaran ƙarya na hotuna da na bidiyo. Abin haushi da takaicin shi ne mutane ba su tsayawa su tantance labari, kawai sai su rubuta a shafukansu, domin neman mabiya, wasu kuma burinsu shi ne a ce su ne suka fara ba da labarin kuma akasarin labaran na ƙarya ne. Ya kamata mu riƙa sanin irin abubuwan da za mu riƙa sanya wa a shafukanmu, kada jahilci ya riƙa ɗibarmu wajen yaɗa labaran ƙarya ko kuma ɓata wa wani suna. To wai…
Read More
Tunatarwa ga talakawan Nijeriya

Tunatarwa ga talakawan Nijeriya

Assalam, ta wannan dama zan faɗa wa talakawa ’yan uwana mafita saboda ra’ayina ba irin naka ba, kila muna da bambancin ra’ayi, abin da zai amfani ƙasata, al‘umar ƙasata banda wata ƙasa da ta fi Nijeriya, ko ina naje ni ’yar ƙasar nan ce Nijeriya. ‘Yan uwa mu tausayawa junanmu mu gina ƙasarmu da zuciya ɗaya, mu zamanto a dunƙule, kunga in mun bi tafarkin nan mun huta, kuma ga siyasa duk da iskar dimukuraɗiya muke ciki mu bayyana wa shugabanninmu kokenmu. Daga Khadija Alhasan. 07036570828.
Read More
Shin farafaganda za ta iya raba Arewa?

Shin farafaganda za ta iya raba Arewa?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Yankin Arewacin Nijeriya ne ka da mafi yawan jama’a a ƙasar Nijeriya mai fiye da mutum miliyan 200. Hakanan yankin na da mabiya addinin kama da musulunci, Kirista, gargajiya da ma wazanda su ka ayyana cewa ba su yarda akwai Allah ba. Daɗin abun tsarin mulkin Nijeriya ya ba wa kowa dama ya yi addinin da ya ga zai fishshe shi. Wannan karo ina son magana ne kan masu neman fakewa da ƙabilanci ko shigar burtu ga addini wajen neman kawo fitina a wannan yanki mai albarka. Tabbas a cikin addinan gargajiya a yankin akwai maguzanci…
Read More
Sauyin Jam’iyya: Mene ne makomar dimukraɗiyyar Nijeriya?

Sauyin Jam’iyya: Mene ne makomar dimukraɗiyyar Nijeriya?

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  ’Yan Nijeriya da sauran manazarta harkokin siyasa na ganin yadda ’yan siyasar ƙasar nan musamman gwamnoni, sanatoci, ’yan majalisu, da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa ke tururuwar canjin sheƙa daga jam’iyyun da aka zaɓe su akai zuwa jam’iyyar APC mai mulki, ko wasu manyan jam’iyyun adawa, alamu ne dake nuna cewa Nijeriya ta doshi zama ƙasa mai jam’iyya ɗaya, a wani ɓangare na shirye-shiryen tunkarar Babban Zaɓen shekarar 2027. A halin yanzu, ana ganin tsarin dimukraɗiyyar Nijeriya na fuskantar sauyi mafi girma, inda jam’iyyu da dama ke rasa ƙarfinsu, wanda hakan ke haifar da tambayoyi…
Read More
Haɗin kan sojojin Nijeriya da Faransa: Ma’anar ziyarar Janar Charpy zuwa NDA

Haɗin kan sojojin Nijeriya da Faransa: Ma’anar ziyarar Janar Charpy zuwa NDA

Daga SENATOR IROEGBU Ziyarar da Laftanar Janar Emmanuel Charpy, kwamandan École Spéciale Militaire de Saint-Cyr (ESM) ta Faransa, ya kai Kwalejin Horar da Sojoji ta Nijeriya (NDA) da ke Kaduna, ta fi zama wata al’ada ta diflomasiyya kawai. Tana ɗauke da ma’ana mai zurfi ga tsaron ƙasa, haɗin kai da matsayin Nijeriya a fagen soja na duniya. A zamanin da ake gaggawar siyasantar da hulɗa tsakanin ƙasashe, ya zama wajibi a fahimci irin wannan ziyara a matsayin girmamawa da haɗin kai, ba nuna rauni ko dogaro ba. Wannan haɗin gwiwa tana nuni da ƙarfin Nijeriya da kuma ikon ta na…
Read More
Duniyoyin rukunin Ranarmu (Solar System)

Duniyoyin rukunin Ranarmu (Solar System)

Daga ALI ABUBAKAR SADIK Sulaiman M. Sani ya turo min da tambayar cewa, shin ko akwai wani nassi na ƙur’ani da ya zo da bayanin duniyoyi takwas da suke wannan rukunin na Ranarmu, wato ‘Solar System’? Haƙiƙa Qur’ani ya zo da bayanin duniyoyi da ke cikin rukunin Ranarmu, kuma bayanin ya zo da wata irin gwaninta ta ilimi, domin Allah ya kauce wa ambatar adadin wadannan duniyoyi. Gwanintar hakan na tattare da cewa wadannan duniyoyi da daya da daya aka rika gano so. A zamunan baya, mutane sun san duniyoyi guda biyar ne kawai wadanda ake iya hangensu, wato—Mercury, ɓenus,…
Read More
Ƙasashen Afrika 11 da Nijeriya ta taimaka ta hanyar tsoma bakin soji

Ƙasashen Afrika 11 da Nijeriya ta taimaka ta hanyar tsoma bakin soji

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ko da Nijeriya ba ta samu sunan “Gwamnatin Afrika” ba, saboda yawan jama’a ko girman tattalin arzikinta kaɗai ba, duk da haka a tsawon shekaru ta kafa tarihin shiga lamarin ƙasashen Afrika duk lokacin da dimokuraɗiyya, zaman lafiya ko tsaron jama’a suka fuskanci barazana. Tsarinta na tsoma bakin soja ya sake fitowa fili a baya-bayan nan, lokacin da ta tura dakarunta ƙasar Binin domin daƙile yunƙurin juyin mulkin da sojoji suka taso da shi. Wannan ba sabon abu ba ne — akwai dogon jerin ƙasashen da Nijeriya ta shiga don taimako. Ga cikakken tarihin ƙasashen da…
Read More
Yadda Ali Nuhu maida ’yan Arewa saniyar ware a Hukumar NFC – Ƙungiyoyi

Yadda Ali Nuhu maida ’yan Arewa saniyar ware a Hukumar NFC – Ƙungiyoyi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Haɗaɗɗiyar ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya a Kannywood (MOPPAN) da haɗin gwiwar ƙungiyar ’Yan Fim ta Arewa (AFMAN) sun nuna damuwa kan yadda ake ƙoƙarin mayar da su saniyar ware a harkokin Hukumar Kula da Finafinai ta ƙasa (NFC) tun bayan da Jarumi Ali Nuhu ya zama shugaban hukumar. A wata wasiƙa zuwa ga shi Darakta Manaja na NFC, Ali Nuhu, wacce Shugaban MOPPAN fitaccen jarumi kuma shugaban MOPPAN na ƙasa, Shehu Hassan Kano da Shugaban AFMAN kuma fitaccen furodusa Salisu Mohammed Officer suka rattaɓa wa hannu, ƙungiyoyin sun bayyana damuwarsu bisa yadda…
Read More
Ba ni ke kashe kuɗaɗe kan matsalar tsaro a Zamfara ba, inji Kwamishinan tsaron jihar

Ba ni ke kashe kuɗaɗe kan matsalar tsaro a Zamfara ba, inji Kwamishinan tsaron jihar

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Kwamishinan ma'aikatar tsaro ta Jihar Zamfara, Amb. Bala Mairiga, ya musanta raɗeraɗin dake yawo a kafafen yaɗa labarai cewar gwamnatin jihar tana basu kuɗaɗe don magance matsalar rashin tsaro a fadin Jihar. Kwamishinan yayi wannan tsokaci ne a wani faifan bidiyo a lokacin da yake ganawa da alummar garin sa na Talata Mafara. Inason wannan faifan bidiyo a yaɗa shi kowa yasan halin da ake ciki, cewar ni babu hannun ma'aikata ta akan yadda ake kashe kuɗaɗe kan matsalar tsaro ". Inji shi. Ya tabbatar da cewar gwamnatin jihar Zamfara tana iya ƙoƙarin ta wajen…
Read More