Duniyoyin rukunin Ranarmu (Solar System)

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIK

Sulaiman M. Sani ya turo min da tambayar cewa, shin ko akwai wani nassi na ƙur’ani da ya zo da bayanin duniyoyi takwas da suke wannan rukunin na Ranarmu, wato ‘Solar System’?

Haƙiƙa Qur’ani ya zo da bayanin duniyoyi da ke cikin rukunin Ranarmu, kuma bayanin ya zo da wata irin gwaninta ta ilimi, domin Allah ya kauce wa ambatar adadin wadannan duniyoyi.

Gwanintar hakan na tattare da cewa wadannan duniyoyi da daya da daya aka rika gano so. A zamunan baya, mutane sun san duniyoyi guda biyar ne kawai wadanda ake iya hangensu, wato—Mercury, ɓenus, Mars, Jupiter da Saturn—har sai bayan da Lippershey ya kirkiri na’aurar hangen sararin samanjya (Telescope) a shekarar 1608 sannan aka fara iya hangen duniyoyi masu nisa.

An fara da gano duniyar Uranus a 1781 wadda William Herschel ya gano. Sai kuma a ka gano duniyar, Neptune a shekarar 1846, duk da dama an yi hasashen layin da ta ke bi. Sai kuma a shekarar 1930, ta hanyar dodon-hoto (photographic plates) aka gano duniyar Pluto. Kirkirar na’urar hangen sararin samaniya ya kawo gagarumin canji a nazarin taurari, yadda ake iya ganin halittun sammai da a baya ba’a iya ganinsu.

To amma a shekarar 2006 sai kungiyar al’amuran nazarin sararin samaniya (The International Astronomical Union) su ka cire Pluto daga jerin duniyoyi 9, aka maida su zuwa 8. To a yan shekarun nan kuma sai ga shi ana ta farautar wata sabuwar duniyar da ake wa lakabi da Planet-ɗ, har yanzu dai ba’a iya tabbatar da ita ba amma kuma shaidu na zahiri na dada karfafa samuwarta saboda tasirin maganadisun da ke motsa abubuwa a yankin da ake zaton ta ke.

Kamar yadda na yi bayani a baya, Allah ya nuna gwanintar ƙur’ani wajen kaucewa bada adadin duniyoyi a wannan rukunin namu, amma sai yayi amfani da yanayin yadda za’a iya hangen wadannan duniyoyi cikin Suratul Takwir.

A cikin Suratul Takwir ayoyi na 15-16 su na maganar planets ne, amma akasarin masu tafsir a baya suna fassara su da taurari, kasancewar yawanci masu fassarar basu da ilimin astronomy ne ya jawo haka. Amma idan aka yi nazarin Ayoyin sosai za’a gane cewa planets Allah ke magana domin ya na bayanin phases na moɓement dinsu yadda wanda ke kan doron Duniya zai gani. Kalmar da Allah ya yi amfani da ita a bayanin ita ce “Khunnus” wadda ke nuna motsi.

Ayar ta raba planets zuwa; Q81:15 “Ba sai na yi rantsuwa da duniyoyi matafa ba (su na komawa baya)”

To, a cikin jerin duniyoyi na rukunin mu wadanne ne su ke irin wannan motsi? Idan ka kalli duniyoyin Mercury da ɓenus, wadanda su ka fado cikin da’irar da Duniya ke kewayen Rana (Earth orbital diameter) wadannan Duniyoyi sun fi duniyar mu kusantar Rana, kuma idan su na bayan Rana lokacin kewayensu, sai mu Hange su kamar Wata, saboda kusurwar (Angle) Earth-Planet-Sun na karuwa sai mu rika ganinsu su na cika a hankali. Yayin da kusurwar ta kai 90° sai su yi rabi. Sai su yi ta karuwa har sai sun cika kamar dai yadda Wata ke yi (Phases). Daga nan kuma sai su fara bacewa har a daina hangensu. Wannan ya yi daidai da bayanin duniyoyi masu tafiya suna dawowa baya.

Sai kuma ayar ta ci gaba da cewa; Q81:16 “…(Duniyoyi) masu gudu (a mike).

Duniyoyin da kuma su ke a wajen da’irar da Duniya ke kewayen Rana, babu yadda za’a yi kusurwar (Angle) na Earth-Planet-Sun ya taba zama 90°, don haka su a koyaushe wanda ke doron Duniya zai iya hango su. Idan muka duba jerin irin wadannan duniyoyi za mu ga cewa duniyar Mars a koyaushe kusan rabin ta ya na ganuwa sannan kuma ita ma duniyar Jupiter ana iya hangenta a koyaushe duk da cewa saboda nisanta daga Duniya ya kai kilomita miliyan 790, dushi-dushi mu ke ganinta. Wannan ayar ke nufi da cewa suna gudu a mike, domin ana ganinsu ko yaushe.

Sai kuma ayar ta karkare da bayanin cewa; Q81:16 “…(Da duniyoyi) su na buya.”

Wato ragowar duniyoyin da su ke nasu zagayen a wajen da’irar da Jupiter ke nata kewayen, ba ma iya ganinsu kai tsaye. Wadannan duniyoyi su ne na – Saturn, Uranus, Neptune, da Pluto (wadda aka cire daga jerin), da ma duk wata Duniya da zamu iya ganowa nan gaba kamar Planet-ɗ. Saboda nisansu daga Duniya sai dai ta hanyar na’urar hangen sararin samaniya mu ke iya ganinsu, kaga sun amsa bayanin ƙur’ani da ya kira su da duniyoyi masu buya ko?

Don haka wajibi ne masana su zage damtse wajen nazarin Ilimin kimiyya sosai, domin wallahi duk yadda ka kai da ilimi, idan baka san kimiyya ba, to kusan kashi 50% na buwaya da gagarar ubangiji zata wuce ka. Kuma mu fa gane cewa ita kimiyya ba aikin Turawa ba ne, asali ma musulmi ne su ka assasa ta, musamman shi Ilimin sararin samaniya, domin a Bagadaza ne karkashin mulkin Harun Al Rashid da dansa Al Mamun aka fara kafa harsashin nazarinta a zamanance. Domin a nan ne karkashin masanin Ilimin lissafi Al Khwarizmi shugaban cibiyar ‘Baitul Hikima” aka fara gina hasumiyar nazarin taurari ta farko ta zamani a duniya (obserɓatory) wadda aka kira da Shamsiyya.

Kimiyya tamkar ‘blueprint’ ce ta yadda Allah ya gina halittunsa masu rai da marasa rai, aikinmu kawai shine, mu yi nazari domin gano yaya tsarin yake wanzuwa, kuma duk wanda ya duƙufa, walau Musulmi ko kafiri, zai iya gano yadda tsarin yake. Barci da Musulmi suka yi sakamakon watsi da ilimi da raja’a wajen komawa kan salaf kawai, shine ya jawo Turawa suka sace Ilimi, suka bar mu da rikice-rikecen aƙida.

Matasa a farka daga barci. Allah ya iya mana, ya ganar da mu baki ɗaya.

Malam Ali manazarci ne mazaunin Kano. Za a iya samun sa a +2348039702951

By ukarofi