Shin farafaganda za ta iya raba Arewa?

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Yankin Arewacin Nijeriya ne ka da mafi yawan jama’a a ƙasar Nijeriya mai fiye da mutum miliyan 200. Hakanan yankin na da mabiya addinin kama da musulunci, Kirista, gargajiya da ma wazanda su ka ayyana cewa ba su yarda akwai Allah ba. Daɗin abun tsarin mulkin Nijeriya ya ba wa kowa dama ya yi addinin da ya ga zai fishshe shi. Wannan karo ina son magana ne kan masu neman fakewa da ƙabilanci ko shigar burtu ga addini wajen neman kawo fitina a wannan yanki mai albarka. Tabbas a cikin addinan gargajiya a yankin akwai maguzanci wanda ya na da tsohon tarihi wataƙila tun gabanin shigowa da ƙarfin addinin Musulunci. Na ga wasu na neman cillawa duk wanda ba ya cikin wani addini da cewa maguzanci ya ke yi alhali shi ma maguzanci addinin ne mai zaman kan sa.

Haba ai sai mai sauya akalar zance zuwa jayayya ko rashin sanin tarihi zai ce maguzanci ba addinin Maguzawa ba ne. Zan nanata har gobe Maguzawa na nan kuma su na gudanarda addininsu na maguzanci. Idan akwai wasu masu wani addinin daban a wani yankin duniya sai a ayyana su da sunansu kamar ‘yan Hindu, Budda da sauran su. Don ka na musulmi ko kirista ba ka da hurumin ɗaukar sunan addinin wasu ka makawa wasu. Na kawo sunan da Allah ya ayyana wasu da ba su yi imani ba da MUSHURKAI. Idan wani da ya yi abun bahaguwar fahimta ya ce MUSHURKAI kalmar Larabci ce sai na ce ai kusan duk wata sadara a rubutun nan na dauke da Larabci kuma MUSHURKAI na yi wa Allah kishiya ne a wajen bauta. A na su ɓangaren Maguzawa su na da allansu GIJI kuma ba sa yi ma sa shirka. 

Sabon zamani ya kawo mu inda Maguzawa su ka fi shiga addinin kirista in za su kara ko sauya addini don ƙaunar su ga Turawan mulkin mallaka waɗanda su ka yaki Daular Shehu Mujaddadi da ya takura mu su da musulunci. Bamaguje ba zai rayu ba tsafi ba don haka ba zai yi walwala ba a cikin musulunci. 

Na ga wasu na kawo hotunan wasu da su ka shiga addinin kirista a matsayin wai su ma Maguzawa ne, wannan zalunci ne don mutum in ya shiga Kirista to addininsa Kiristanci ne ba maguzanci ba. Maguzanci addinin Maguzawa ne na bori, tsafi da hulda da dodanni da aljanu ƙarƙashin GIJI uban giza-gizai. 

Hausawa musulmi ba su da hulɗa ko babbar alaka da Maguzawa don tun tale-tale an tsame maida al’adunsu na musulunci kuma Hausa na daga manyan harsunan Musulunci. 

Na yi bincike na ga tabbas masu iƙirarin Hausa zalla na yin abun da su ka ga dama ne saboda sun raba hanya da tarbiyyar addini kuma ba sa kaunar Hausawa don ƙarfin Musuluncin Hausawa a duniya. Babban muradin ‘yan kwangilar Hausa zalla shi ne haddasa fitina tsakanin musulmi a wayi gari Musulmi su na ɗauki ba dadi a tsakaninsu. Wannan irin fitina ta faru a tsaunin Mambilla inda illar kiyayyar ƙabilanci ta sa a ka yi ƙazamin faɗa a tsakanin Musulmi. Yayin da mabiya addinin Kirista na kamfen ɗin Hausa zalla su ka fito har da naɗa sarkinsu a babbar masarautar Kano, an samu adawa daga ‘yan uwansu Maguzawa da ke ganin wannan ba zai cimma burin muradin da su ke aiki dare da rana a kai ba. Ai ba laifi musulmi zai iya rayuwa da Kirista don haka a ke zaune a Nijeriya.

Asalin Maguzawa masu bin addinin maguzanci ƙarƙashin babban allansu GIJI da allarsu Doguwa sun fi son a cigaba da gashi a na zuga mutane su rungumi kiyayyar ƙabilanci don ta nan ne a na tsakiyar sallah a masallaci wani zai ce ai liman ɗan ƙabila kaza ne mu cire shi mu nada ɗan ƙabilarmu. Daga nan za a shiga dauki ba daɗi har ya kai ga an fara yaƙi shikenan sai miyagun su hau soshiyal midiya su yi ta ruruta wutar ta hanyar zuga ɓangarorin biyu ta hanyar logar annamimanci. Ba lallai an san su ba ma don sunayen karya da hotunan karya su ke amfani da su. Wasu ma na gantali a ƙasashen ƙetare inda wasu ke jihohin Arewa ta tsakiya da Arewa maso gabar. Burin fitina ta turnuƙa can kokuwar Arewa.

Aikin karantarwa na Shehu Usumanu da ƙarfafa Musulunci gam-gam ya yi wa irin waɗannan Maguzawa illa don su dama ba za su taba karɓar Musulunci ba amma da yawansu da Bature ya shiga Daular Sokoto daga 1903 sun shiga addinin Kirista don ba zai hana su bori, tsafi da shayar da dodanni jini ba. Abun da ke Konawa Bamaguje rai shi ne ya ji an rangaɗa kiran sallah wannan ma, na daga dalilin da ya sa wasunsu komawa ƙauyukan gefen birane su na noma. Hakan ba wai don son zaman lafiya ba ne, a a rashin son jin kiran sallah ne da ganin giftawar Musulmi.

Hatta gaisuwar addinin Musulunci ta ASSALAMU ALAIKUM ba sa kauna sai AHO KUM ko AHUWANKU DAI MASU GIDAN NAN. Da dai Turawan mulkin mallaka sun samu sun canjawa Musulmi addini zuwa addinin Nasara, da Maguzawa sun ajiye kiyayyar su ga Shehu. Yau duk wanda ka ga ya zagi Shehu za ka same shi wa in ma mugun mabiyin addinin Kirista ne da bai damu da koyarwar BIBLE ba ko Bamaguje ne mai bin Giji. Idan ka dan motsa kadan wai ko ka ga wasu na kama da musulmi ko har su na iya jan ayoyin Alkur’ani har ma da masu zuwa aikin hajji, tabbas za ka taras ‘yan logar sadaka-yalla ne mu na bara mu na karuwa wato su na da dangin kusa da Maguzawa makiya Shehu da addinin da Shehu ya jaddada.

Nan gaba Insha Allah zan yi bayani ga sahihin labarin da ke tabbatar da an tura wasu Maguazawa ƙasashen Larabawa sun koyo Larbaci wasu ma har su kan haddace Alkur’ani, amma don cimma muradin makiya Musulunci ne da Arewa. An turo miyagun su na ta ruruta wutar fitinar kabilanci da nuna kabila ta fi addini.

Yanda mu ka haska Ouba Ali Mohaman na Kamaru uban ‘yan kwangilar rusa Arewa da yayyafa ruwa a Kamaru, za mu fito da bayanai filla-filla kan sauran miyagu masu ɗaukar nauyin lalatacciyar hanyar nan ta kirista ba BIBLE da Maguzanci Sak Musulunci Sam.

Addinin Musulunci ya haramta ƙabilanci don haka duk wanda ya zama Musulmi bai halalta ya bari ƙabilanci ko na kwayar zarra ya shiga zuciyarsa ba. ‘Yan ta’adda ko ɓarayin daji da a ke magana ba sa wakiltar kowace ƙabila sai kan su kaɗai. Kakaf ‘yan ta’adda nawa ne ke wannan mugun laifi? Shin tsakani da Allah wa ya tsira daga barazanar ‘yan ta’adda? Wanene ba su taba sacewa ba?. Duk wanda ya ayyana ɓarayin daji da wai su na yin hakan ne kan doron ƙabilanci to azzalumi ne, ba ma irin mai fakewa da wannan dama wajen zagin Mujaddadi Shehu Usumanu Danfodiyo. Wallahi duk zafin fitina da ka gani wataran za ta kawo ƙarshe. An yi yaƙin duniya na ɗaya an yi na biyu kuma har yau duniyar na nan.

Na ga akasarin mutane na nuna farin ciki bisa naɗa tsohon babban hafsan soja Janar Christopher Musa a matsayin ministan tsaro. Mu na fata Allah ya ba shi dama ta tsara manufofin tsaro don dawo ma na da zaman lafiya mai ɗorewa. Haƙiƙa ƙalubalen tsaron ya wuce surutan nan na yanar gizo, don ba a tonawa kawai saboda hatsarin fito da bayanai masu tsauri, amma alamu sun nuna sam-sam masu farafagandar Hausa zalla ba sa kaunar a samu zaman lafiya don cigaba da fitinar ne zai ba su damar kunna ta su wutar ta yaƙin ƙabilanci inda za su haɗa Musulmi yaƙi tsakaninsu, sai su koma gefe su kunna kidan Bob Marley su yi ta tikar rawa a wasu kauyukan su da ba a samun masu tsawatawa. Duk nuna goyon baya da su ke yi wa Janar Musa ka iya zama munafurci kawai, haushin naɗin su ke ji. Ai gwamnati kan yi sauyi ko garambawul a jami’ai ko a majalisa ministoci don ƙara inganta aiki. A nan mun san ba wata shaida da gwamnati fitar da ke nuna gazawar tsohon ministan tsaro Alhaji Muhammad Badaru, hasalima fadar Aso Rock ta ba da labarin shi ya yi murabus da kan sa don dalilan rashin ƙoshin lafiya. Kamata ya yi ‘yan Nijeriya su haɗa kai don zaman lafiya ya fi komai alheri.

KAMMALAWA

Haƙiƙa Musulmi ba za su yi yakin ƙabilanci ba don addinin Musulunci ya haramta hakan. Da zarar Ladan ya kira sallah kowa zai yi alwala ya amsa kira ɗaya tal. Allahu Akbar Allahu Akbar. Ku duba miliyoyin Musulmi da ke taruwa a aikin hajji amma da zarar an tayar da sallah kowa sai ya natsu ya bi liman, ba bambancin ƙabila ba na launin fata. Allah mun gode ma ka.

Babban dillalin makiya Nijeriya ta Arewa Ouba Ali Mohaman ya sa an tara kirare, ya na feso fetur daga Kamaru don jiran jin rakas-rakas ya kyasta ashanar yakin ƙabilanci. Albishirinka mugu, da zarar ka kyasta ashanar wutar za ta juya ta kona ka ƙurmus. Mu na kira ga musamman Musulmi da Kirista a Arewa su haɗa kai su zauna lafiya kowa ya riƙa gudanarda addininsa ba tsangwama ba hararar juna da bahaguwar manufa.

By ukarofi