Da ɗumi-ɗumi: Mahara sun kashe wata mata mai juna biyu da ɗanta mai watanni 18 a Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Al’ummar yankin Sheka Sabuwar Gandu da ke ƙaramar hukumar Kano Municipal sun shiga firgici da tashin hankali, bayan wasu da ba a san ko su wanene ba sun kashe wata mace mai juna biyu tare da ɗanta mai wata 18.

Lamarin ya faru ne a daren Asabar, lokacin da mijin mamaciyar ya dawo gida daga wurin aiki da misalin ƙarfe 8:00 na dare, inda ya tarar da ƙofar gidansu a kulle.

Rahotanni sun nuna cewa mijin, wanda aka ɓoye sunansa saboda dalilan tsaro, ya tambayi maƙwabta bayan ganin gidan a kulle. Sai aka shaida masa cewa matarsa ba ta fita ko’ina ba.

Daga nan ne ya tilasta shiga gidan, inda ya yi arangama da gawar matarsa da ɗansu a wani yanayi mai tayar da hankali.

Daga bisani, mazauna yankin suka sanar da hukumomin tsaro game da aukuwar lamarin.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban al’ummar yankin, Ahmad Sani, ya ce mazauna yankin sun kaɗu matuƙa da abin da ya faru, inda suka gaggauta zuwa wajen da abin ya auku bayan samun rahoto.

Kzalika, ya nuna damuwa kan ƙarancin jami’an tsaro a yankin, yana mai cewa duk da cewa an gina ƙaramin ofishin ‘yan sanda a baya, har yanzu ba a tura jami’an tsaro domin gudanar da aiki a wurin ba.

Sannan Mallam Sani ya yi kira ga Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Dr. Ibrahim Adamu Bakori, da ya ɗauki matakin gaggawa ta hanyar ƙarfafa tsaro a yankin, domin hana faruwar makamantan hare-hare a nan gaba.

Jaridar Telegraph ta ruwaito cewa, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai yi cikakken bayani ba kan lamarin, inda ya ce bincike na ci gaba da gudana.

By ukarofi