Takunkumin da Amurka ta kakaba kan manyan kamfanonin man Rasha, Lukoil da Rosneft, na iya janyo babban sauyi a taswirar man duniya a shekara mai zuwa, lamarin da zai daƙile tasirin da Rasha ta daɗe tana samu a kasuwannin duniya.
Takunkuman, waɗanda suka fara aiki a ranar 21 Nuwamba, sun daɗa rage kuɗaɗen shiga da Rasha ke samu daga man fetur — wanda yake raguwa da kusan kashi ɗaya bisa uku.
A yanzu haka, kasashe kamar Turkiyya, Indiya da Brazil sun rage sayan man Rasha, lamarin da ya bar dubban ganga suna lilo a tekuna ba tare da mai saye ba. Masana sun ce Rasha na iya tilas ta sayar da man da farashi mai matuƙar sauki ga Chana.
ƙasashen gabashin Turai na saurin rabuwa da tasirin Lukoil, inda gwamnati a Bulgaria ta karɓi ikon tsarin kamfanin. Romania da Moldova suma sun dauki matakai na kawar da rikon Rasha.
Hungary da Slovakia ne kawai ke ci gaba da karɓar man Rasha ta bututun Druzhba, amma akwai hanyoyin maye gurbinsu.
Takunkumin na tilastawa Lukoil sayar da ƙadarorinta na ƙasashen waje kafin wa’adin 13 Disamba, ciki har da wuraren hakar mai a Iraƙ, Kazakhstan, Azerbaijan, Mexico da Afirka.
Masana sun ce wannan zai iya canza yadda ake zuba jari a kasuwar makamashi tsawon shekaru masu zuwa.
