Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Shugaban ƙaramar Hukumar Gwaram da ke jihar Jigawa, kuma Shugaban ƙungiyar Shugabannin ƙananan Hukumomi na Nijeriya ALGON, reshen jihar Jigawa, Farfesa Abdurahman Salim Lawan, ya ce a ƙaramar hukumarsa ta Gwaram abun da ke faranta masa rai shi ne tsarin bai wa ɗaliban ƙaramar hukumar kayan makaranta kyauta, tallafin marayu da aikin gina makarantun firamare 11 da aikin rijiyar burtsatse mai aiki da hasken rana 11 da masallatan Juma’a 11 da ayyukan magudanar ruwa domin kaucewa ambaliyar ruwa duk da goyon bayan gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ɗanmoɗi, “saboda nagartarsa da kishin ƙasar sa abun a yaba masa ne da sauran ayyuka na cigaban Jigawa ta kowanne fanni na rayuwa,” kamar yadda shugaban ALGON na Jigawa ya bayyana.
Haka kuma ya bayyana ayyukan cigaban Jihar Jigawa da Gwamna Malam Umar Namadi ɗanmoɗi ya yi tsari ta yadda nan da ɗan lokaci kaɗan da ikon Allah Jigawa za ta noma shinkafa kashi 25 cikin 100 na shinkafar da Nijeriya take buƙata a noma duk shekara.
Farfesa Abdurahman ya ƙara da cewa Gwamna Malam Umar Namadi ɗanmoɗi ya yi tsari na samar da ton 300 wanda kowace mazaɓar ɗan majalisar jiha za ta samu ton goma, sai kuma ƙari da za a bai wa hamshaƙan manoma ƙari akan 300 na mazaɓu ƙananan hukumomin jihar 27 sai kuma shirin tallafawa manyan manoma 1000 da za su noma hekta ko kadada 500 a jihar ta Jigawa, akwai tsarin tallafawa manoma 200 a kowacce ƙaramar hukuma ta jihar ta hanyar ba su tallafin kayan aikin noma kamar haro da rijiyoyin burtsatse na noman rani da sauransu, ga kuma matasa da aka tura Abekuta koyon noman zamani irin Turai ga kuma tallafi da shirin bunƙasa noman alkama na Gwamna ɗanmoɗin Jigawan da sauransu.
Har ila yau Hon. Abdurahman Salim Lawan ya ƙara da cewa a ƙoƙarin gwamnan na samawa matasa aikin yi yanzu haka an horar da mata sama da dubu 100 ɗinkin hula na zamani da kuma tallafi da za a ba su da kayan aiki don bunƙasa sana’o’in gado, sai matasa da aka horar kasuwancin zamani da buɗe musu wurin karɓar kuɗi ko bada ko bada kuɗi POS da aka yi wa laƙabi da ɗanmoɗi KIYOS da dai sauransu.
Haka kuma ya bayyana cewa gwamnatin Jigawa ta ɗanmoɗi a ɓangaren bunƙasa ilimi an ɗauki malaman makaranta 6233 don bunƙasa ilimi haka ta mai da ilimin mata tun daga firamare har zuwa digri na uku kyauta, haka su ma ɗalibai maza kan samu tallafin dubu 70 na tallafin karatu inda su ke yin rijistar karatu ƙasa da dubu 20 haka abun yake a ɓangaren lafiya ta yadda al’ummar Jigawa manoma har ma’aikata da suka samu ƙarin albashi kashi 120, da sauran al’ummar jihar ke cin gajiyar tallafin lafiya na gwamnan Jigawa.
