Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Mali, Assimi Goita da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar makamashin nukiliya a fadar Kremlin da ke birnin Moscow.
Wannan dai na cikin wasu yarjejeniyoyi da Mali da Rasha suka rattaba hannu waɗanda aka tsaro domin inganta alaƙar kasuwanci da tattalin arziki.
Shugaba Vladimir Putin ya shaida wa shugaban ƙasar ta Afirka ta Yamma da ke ziyara cewa akwai wasu fannoni na musamman da za a iya ƙara haɗin kai.
Putin ya karɓi baƙuncin Kanal Assimi Goita a fadar Kremlin, inda suka tattauna tsawon awanni biyu, kamar yadda kafafen yaɗa labaran gwamnati na Rasha suka bayyana.
Putin ya ce dangantakar Rasha da Mali tana samun “kyakkyawan ci gaba” duk da cewa cinikayyar ɓangarorin biyu a halin yanzu tana da “ƙaranci,” kamar yadda rahoton Kremlin ya nuna.
Daga cikin abin da yarjejeniyar ta ƙunsa akwai haɗin kai domin samar da makamashin nukiliya, kamar yadda Rashar ta bayyana.
Goita dai yana ƙara ƙulla alaƙa da Rasha ne bayan juyin mulkin da ya jagoranta a shekarar 2021, sannan ya juya wa Faransa — wadda ta raini ƙasarsu baya.
Da yake jawabi a ranar Litinin, Putin ya ce sun inganta yarjejeniyar ne, sannan suka tattaunawa hanyoyin da za su ƙara ƙulla alaƙa a “ɓangarorin ma’adinai da makamashi da agaji.”
Goita ya yi godiya ga Rasha bisa irin “karamcin” da aka masa, sannan ya nanata shirin Mali na ɗabbaƙa yarjejeniyar, waɗanda ya ce sun ƙunshi ɓangarori da dama.
Alaƙar tsaro dai na cikin muhimman abubuwan da ke tsakanin Rasha da Mali.
