
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce gwamnatinsa na da damar sanin duk ayyukan da ’yan bindiga da ’yan ta’adda ke yi a jihar, ta hanyar amfani da tauraron ɗan-adam da jiragen sama marasa matuƙa, wato drones.
A wata hira da manema labarai a Gusau, gwamnan ya bayyana cewa, ana tura waɗannan bayanai kai-tsaye ga dukkan hukumomin tsaro da abin ya shafa, ciki har da ’yan sanda, sojoji, hukumar DSS da Civil Defence.
Saidai gwamnan ya nuna takaici matuƙa, inda ya ce duk da samun waɗannan bayanai akan lokaci, hukumomin tsaro ba sa ɗaukar matakin da ya dace domin dakile hare-haren.
A cewarsa, “da zarar kana da kayan aiki da bayanai, ba abu ne mai wahala a dakile wadannan ’yan ta’adda ba, domin suna rayuwa ne a cikin al’umma.”
Gwamnan Zamfara ya tambayi yadda zai yiwu a ce ’yan bindiga ko ’yan ta’adda sun fi ƙarfin gwamnati, yana mai jaddada cewa hakan ba zai yiwu ba idan ana amfani da kayan aiki da bayanai yadda ya kamata.
Ya ƙara da cewa, abin takaici ne yadda ake barin waɗannan bayanai ba tare da ɗaukar mataki ba, lamarin da ke kara jefa al’umma cikin fargaba.
Dauda Lawal ya kuma ce ya gana da Shugaba BolaTinubu, inda ya bayyana masa a fili halin da ake ciki, yana mai cewa ba a sanar da shugaban gaskiyar halin tsaro yadda ya kamata ba.
Har ila yau, ya ce, ya nuna masa hanyoyin da ya kamata a bi domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro, idan aka ba wa batun fifiko akan muhimman al’amuran ƙasa.
