
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A daren yau Talata ne aka ga watan Ramadana a Saudiyya, wanda ke nuna za a tashe da azumi a gobe Laraba a faɗin ƙasar.
A cewar jaridar Haramain, an ga watan ne a daren Talata wayewar Laraba, wanda kuma ke nuna yau, 17 ga Fabrairu ne ƙarshen watan Sha’aban.
Ana gane watan Ramadana ya fara ne daga Kalandar Hijiriyya ta Musulunci, wadda watanninta ke kaiwa kwanaki 29 ko 30.
Haka kuma, ana kammala azumi ne a watan bisa la’akari da ganin jaririn watan Shawwaal.
A Nijeriya kuwa, al’ummar Musulmi za su saurari sanarwa ta musamman daga Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar na III domin fara nasu azumin.
A jiya Litinin ne, Sarkin, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Ƙolin Shari’a na Harkokin Musulunci a Nijeriya, ya yi kira ga musulmi a ƙasar da su fara duba jaririn wata a yau Talata.


