
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta sake buɗe shari’ar sanannen mai sharhi akan al’amuran gwamnati, Abubakar Idris da aka fi sani da Dadiyata, wanda ya yi ɓatan-dabo a Kaduna a shekarar 2019, da ɓatar wasu mutane da dama da aka alaƙanta su da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i.
Wani babban jami’in tsaro ya bayyana haka, da kuma batun ƙwace fasfon El-Rufa’i a ranar Alhamis ɗin da ta gabata daga jami’an DSS a Filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, inda ya ce an yi haka ne da nufin hana shi zuwa Masar bayan shigowa Nijeriya da wucin-gadi.
A cewar wata majiyar tsaro, an sake tada batun ɓatar Dadiyata ne bayan tsawon watanni ana bincike akan al’amarin nasa, inda ake zargin El-Rufa’i, wanda shi ne gwamna a lokacin, da shirya garkuwa da matashin.
Dadiyata, wanda lakcara ne a tsangayar ilimin harsuna ta Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma, Jihar Katsina, ya ɓata ne a ranar 1 ga watan Agustan 2019 bayan gano wasu ‘yan bindiga sun yi awon-gaba da shi a gidansa na Kaduna, kamar yadda matarsa ta sanar, wanda har zuwa yanzu babu labarinsa.
lDa yake jawabi a ranar Juma’a yayi hira ta gidan talabijin na Arise, El-Rufa’i, wanda shi ne gwamna tsakanin 2015 da 2023 a Kaduna, ya bayyana yadda aka zargi wani ɗan sanda da ya tuba, da yin bayanin cewa yana ɗaya daga cikin “tawagar da aka tura daga Kano domin sace Dadiyata”.
Tuni dai DSS ta tabbatar da cewa ta fara binciken El-Rufai da dansa kan zargin hannu a bacewar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, a shekarar 2019.
