
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Litinin Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta shigar da ƙara tuhume-tuhume guda uku akan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i.
A takardar ƙarar mai lambar FCT/ABJ/CR/99/2026, hukumar ta zargin tsohon gwamnan da yin kutse ba bisa doka ba a wayar Mai bai wa shugaban ƙasa akan harkokin tsaro (NSA) Nuhu Ribaɗu.
Haka kuma ana zargin sa da wasu manyan laifuka bisa kalamansa na ranar 13 ga watan Fabrairu, a wata hira da gidan talabijin na Arise.
A ƙarar, wadda M. E. Ernest ya shigar a madadin DSS, El-Rufai ya tabbatar da cewa shi da wasu makusantansa sun yi kutse a hirar wayar Ribaɗu.
Gwamnatin Tarayya ta yi ikirarin cewa zargin aikata hakan ya saɓa wa dokokin laifukan yanar gizo da na sadarwa, sannan kuma barazana ga tsaron al’umma da ma ƙasa baki ɗaya.
Haka kuma, wasu takardun kotu sun zargi tsohon gwamnan mai shekaru 65 da ƙin kai ƙarar waɗanda suka gudanar da kutsen ga hukumomin da suka dace duk da cewa ana zargin sa da sanin aikata laifin.
A cewar DSS, kutsen wayar Ribaɗu da wani nau’in kayan fasaha abu zai iya dagula al’amura a harkar tsaron ƙasa duba da cewa yana jagorantar ɗaya daga cikin sashen tsaro a Nijeriya.
