Daga USMAN KAROFI a Abuja
Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa (NCDC) ta sanar da cewa an samu sabbin mace-mace guda 13 sakamakon zazzaɓin Lassa cikin makonni biyu da suka gabata. A mako na huɗu na sanya ido kan cututtuka, an samu mutane 189 da ake zargi sun kamu, 28 da aka tabbatar sun kamu, da kuma mace-mace bakwai. Hakan ya kawo jimillar mutane 594 da ake zargi, 121 da aka tabbatar sun kamu, da kuma mace-mace 25 gaba ɗaya.
A mako na gaba kuma, an sake samun ƙarin masu ɗauke da cutar inda aka samu mutane 160 da ake zargi, 44 da aka tabbatar sun kamu, tare da karin mace-mace shida. Duk da cewa hukumar ta ce an samu ɗan sauki kaɗan a yawan mace-mace idan aka kwatanta da makonni biyun da suka gabata, ta bayyana cewa ƙarin waɗanda aka tabbatar sun kamu abin damuwa ne kuma na buƙatar ɗaukar matakan gaggawa.
NCDC ta buƙaci jama’a da ma’aikatan lafiya su bi ƙa’idojin kariya domin daƙile yaɗuwar cutar, ciki har da wanke hannu da sabulu a ƙarƙashin ruwa mai gudana, amfani da sinadarin tsaftace hannu idan hannu bai datti ba, da kuma sanya kayan kariya kamar safar hannu, takunkumin fuska da rigunan kariya. Haka kuma, ta umurci asibitoci su tanadi wuraren killace waɗanda ake zargi da tabbatar da horas da ma’aikata kan yadda za a gano, ware da kuma kula da masu ɗauke da cutar yadda ya kamata.
