Ba a biyan kuɗi saboda aikin kashe gobara, inji hukumar ’yan kwana-kwana

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban Konturola Janar na Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (FFS), Olumode Samuel Adeyemi, ya gargaɗi jama’a cewa jami’an hukumar ba su da hurumin karɓar kuɗi kafin, lokacin ko bayan gudanar da aikin kashe gobara.

Ya kuma buƙaci duk wanda wani jami’in hukumar ya nemi kuɗi daga gare shi da ya kai rahoto ga hukumar domin ɗaukar matakin ladabtarwa cikin gaggawa.

Adeyemi ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja ranar Laraba, inda ya jaddada cewa duk jami’in da aka kama da irin wannan ɗabi’a zai fuskanci hukunci mai tsauri.

Ya ce, ba jami’in kaɗai ba ne zai ɗauki alhakin laifin, har da shugaban ofishin kashe gobarar da abin ya faru da kuma Konturolan Hukumar Kashe Gobara na jihar da abin ya shafa.

Babban Konturolan Janar ɗin ya yi wannan bayani ne yayin da yake martani kan wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, wanda aka ce ya fito daga Jihar Ribas, inda aka zargi wasu jami’an kashe gobara da neman kuɗi kafin su kashe gobara.

Sai dai ya bayyana cewa Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya ba ta da ofishi ko jami’ai a wurin da aka ce lamarin ya faru.

Adeyemi ya ce, Gwamnatin Tarayya tana samar wa hukumar duk abin da take buƙata domin gudanar da aikinta yadda ya kamata.

A cewarsa, ana biyan albashin jami’ai a kan lokaci, ana samar da motocin kashe gobara, kayan aiki da sinadaran da ake amfani da su, tare da kula da jin daɗinsu.

Ya ƙara da cewa, ta hannun Ministan Harkokin Cikin Gida, gwamnatin ta kuma tabbatar da cewa babu jinkirin ƙarin girma ga ma’aikatan hukumar.

Ya ce a shekarar 2026, duk ma’aikatan da suka cancanci ƙarin girma sun riga sun rubuta jarrabawar ƙarin matsayi, kuma ana sa ran fitar da sakamakon kafin watan Oktoba.

Saboda haka, ya ce babu wani dalili da zai sa jami’an hukumar su nemi kuɗi wajen gudanar da aikin da doka ta ɗora musu.

Adeyemi ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su gaggauta sanar da hedikwatar hukumar idan wani jami’in kashe gobara ya nemi kuɗi a kowane mataki na aikin kashe gobara.

Ya kuma yi kira ga jami’an hukumar da su ci gaba da gudanar da aikinsu cikin gaskiya, riƙon amana da mutunci.

A cewarsa, duk ofishin hukumar da aka samu da irin wannan laifi za a hukunta shugabanninsa, ciki har da shugaban ofishin da Konturolan Hukumar Kashe Gobara na jihar, inda ya ce za a cire su daga mukamansu tare da ɗaukar matakin ladabtarwa a kansu.

By ukarofi

Leave a Reply