Ba a kama hanyar tsagaita wuta a Lebanon ba!

Kai tsaye daga bayanan da ke fitowa daga gabar ta tsakiya a yaƙin da Isra’ila ke cigaba da yi kan Lebanon, ya fito ƙarara an fahimci ba a ma kama hanyar tsagaita wuta a Lebanon ɗin ba balle ma a je ga batun Gaza. An ga dai yaƙin da ya wuce shekara daya da farawa na kara laƙume rayukan waɗanda ba su ji ba su kuma gani ba. Yaƙin kamar rigar siliki ya zama a saba vari ɗaya sai ɗaya varin ya goce. Masar, Katar har ma da Amurka kan zauna da sunan sulhunta Hamas da Isra’ila amma sai a tashi dutse hannun riga.

Tun a na fargabar yaƙin zai faɗaɗa zuwa wasu yankuna ga shi ya faɗaɗa zuwa Lebanon da Sham kai har ma da hare-hare a Iran da turjiyar houthi a Yaman kan jiragen ruwan ƙasashe masu marawa Isra’ila baya. Waye ma a sanannun jagororin Hamas ya rage ne bayan kashe jagora Isma’il Haniyeh, Yahya Sinwar da kuma can Lebanon shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah.

Ga kwamandoji nan da dama da su ka rasa ran su. In ma ramuwar gaiya Isra’ila ke yi to ya dace ta dakata hakanan. A nan za mu ce zargin kisan kare dangi da Afurka ta kudu ta yi wa Isra’ila ƙarƙashin firaminista Benjamin Netanyahu ya tabbata. Mun tuna fa har kotun duniya a ka kai Isra’ila ƙara don ta tsagaita yaƙin amma ina. Ba kasa ko ɗaya da ta aiyana neman firaminista Netanyahu ruwa a jallo don bijirewa umurnin kotun duniya. Ba wannan ne karo na farko da zan ce Netanyahu ya ma furta kalmomi kushe kotun kuma ba abun da ya faru.

Ai kotun ta yi wa hatta shugaba Vladimir Putin na Rasha barazana duk da zai yi wuya wani abu ya same shi don ƙasar sa na cikin masu nukiliya a duniya ga kuma zama memba ta dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin Duniya. Adalcin duniya na zama iya ruwa ne fidda kai ko duk wanda ya iya allonsa ya wanke. Na kan ɗan leƙa wasu kafafen labaru na wuce a gurgurje don za ka ga hotunan yara kanana ‘yan Falasɗinu lulluve cikin jini a likkafani bayan kisan gilla da a ka yi mu su. In da safe mutum ya kalli irin waɗannan hotuna da zai iya wuni cikin juyayi.

Shi ya sa wani lokacin gara ma ba ka san dukkan abun da ke faruwa ba. Duk yaki da a ke yi akwai ƙa’idar kaucewa kashe yara da mata ko ma dai a ce waɗanda ba su da ɗamarar yaƙi. Isra’ila ta zargi Hamas da gina ramuka a kasan asibitoci da ya zama dalilin ta na kai farmaki a kusan dukkan asibitocin Gaza. Wannan ya nuna in mutum ya samu rauni a ka kai shi asibiti ba lallai ne shi da likitan su kai labari ba don an jima ko gobe za a iya taruwa don juyayin an kashe su. A Gaza fa wata martaba ce ma a samu gawar mutum a ma sa jana’iza, wasu da dama fa su na bunne a kasan gine-gine da jiragen yaƙin Isra’ila su ka yi wa asha ruwan tsuntsaye na boma-bomai.

Sabbin labarun da ke fitowa daga Lebanon da Gaza;

Isra’ila ta kai farmaki a yankin tsakiyar babban birnin Lebanon Beirut inda ta yi kisan gilla ga shugaban labaru na ƙungiyar Hezbollah Muhammad Afif.

Wannan shi ne karo na farko da Isra’ila ke kai hari kan yankin na Ras Al-Naba tun fara zafafa hare-hare kan Lebanon.

Kazalika shi ma mai taimakawa Afif mai suna Mahmud Al-Sharƙawi ya rasa ran sa a irin wannan kisan gilla da ya auku ranar Lahadi.

Hakanan wasu mutum 3 ma sun samu raunuka a farmakin kan yankin mai yawan jama’a da su ka haɗa da waɗanda su ka yiwo hijira daga kudancin Lebanon don gujewa hare-haren Isra’ila.

Jami’an lafiya sun bayyana ganin jini a ginin da Isra’ila ta ruguza kuma su na kara bincike don sanin makomar sauran mutanen da ke cikin ginin.

Jiragen yaƙin Isra’ila sun yi ruwan boma-bomai kan Chiyah da ke kudancin Lebanon inda hakan ya haddasa rugujewar gine-gine da tada gagarumar gobara da hayaƙi.

Chiyah dai na zaman kusan matsuguni ɗaya tak da mutane ke rakuvewa da tunanin Isra’ila ba za ta kai ma sa hari ba a kudancin Lebanon ɗin.

Isra’ila ta gargaɗi mutane rabin sa’a su fice daga yankin kafin ta turo jiragen yaƙi su yi ta sauke boma-bomai.

Mazauna Chiyah na kokawa cewa ba wani dan Hezbollah da ke zaune a garin na su don haka ba su ga dalilin kai mu su wannan mummunan harin ba.

Har yanzu dai Isra’ila na da zummar ruguza dukkan yankunan kudancin Lebanon ko ƙarfin Hezbollah da daidaita ƙungiyar Hamas a Gaza gabanin amincewa da sulhu.

Ma’ana dai Isra’ila na son dakatar da buɗe wuta lokacin da ta gama ruwan wuta ta yadda ba wanda zai sake yi ma ta barazana kan muradun ta na mamaye ƙasar Falasɗinu.

Iran ta nuna goyon bayan neman samun tsagaita wuta tsakanin ƙungiyar Hezbollah da ta ke marawa baya da Isra’ila.

Duk da yunƙurin samun sulhu da Amurka ke son shigowa da shi ta fuskar diflomasiyya, har yanzu Isra’ila na ruwan boma-bomai a kudancin Lebanon da hakan ke ruguzagine-gine da haddasa asarar rayuka.

Hezbollah ta amince kakakin majalisara dokokin Lebanon Nabih Berry ya zama mai shiga tsakani a tattaunawar.

Babban jami’in gwamnatin Iran Ali Larjani ya sauka a Beirut babban birnin Lebanon inda ya gana da Berry ya kuma bayyana goyon bayan samun sulhu.

Duk da al’ummar Gaza da wannan yaƙi ya daidaita fiye da shekara na son a tsagaita wuta, har yanzu Isra’ila ba ta nuna wani tsari mai muhimmanci na samun hakan ba.

Jakadan Amurka Amos Hochstein ya baiyana cewa samun yarjejeniya ta tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hezbollah na daf da samun nasara.

Hochstein ya bayyana haka a babban birnin Lebanon, Beirut bayan ganawa da shugaban majalisar dokokin ƙasar Nabih Berry wanda Hezbollah ta wakilta ya jagoranci yarjejeniyar a madadin ta.

Berry dai dan Hezbollah din ne da ya ɗau zamani kan jagorancin majalisar dokokin Lebanon kasancewar dama tsarin mulkin Lebanon na ɗora ɗan Shi’a a jagorancin majalisa, shugaban ƙasa Kirista yayin da firaminista kan zama ɗan ahlus sunnah.

Jakadan ya gana daga bisani da firaminisa Najib Mikati wanda ya kwan biyu ya na ƙarfafa hanyoyin diflomasiyya don samawa al’ummar sa maslaha daga kutsen isra’ila.

A irin bayanan Hochstein, za a iya cimma wannan yarjejeniya a ‘yan kwanaki kalilan.

Za a yi amfani da tsohuwar yarjejeniyar sulhu tsakanin Isra’ila da Hezbollah ta 2006 lokacin da a ka tava samun fitina.

Kungiyara Hezbollah a Lebanon ta ce sam ba za ta bari abokiyar arangamar ta kasar Isra’ila ta ƙaƙaba sharuɗɗan da ta ga dama kan shirin yarjejeniyar tsagaita wuta ba.

Shugaban Hezbollah Na’im ƙassem ya bayyana matsayar a wani jawabi mai nuna rashin amincewar Hezbollah kan take-taken Isra’ila.

Wannan na faruwa yayin da jakadan Amurka Amos Hochstein ke barin Beirut don tafiya Tel’Aviv ya gana da jagororin Isra’ila.

Ministan wajen Isra’ila Gideon Saar ya ce lallai yarjejeniyar ta kunshi barin Isra’ila ta ɗau mataki ko kai farmaki in ta kama kenan kan Hezbollah.

A nan ƙassem ya ce ba zai yiwu Isra’ila ta tilasta wani sharaɗi ba don haka Hezbollah ba za ta lamunci hakan ba.

ƙassem ya ce dole ne yarjejeniyar ta ƙunshi cikakken ‘yancin Lebanon da dakatar da duk wani farmaki.

Baya ga wannan matsaya, ƙassem ya kuma ce ramuwar gaiya kan mummunan harin da Isra’ila ta kawo Lebanon zai shafi babban birnin Isra’ila ne Tel’Aviv.

Amurka ta hau kujerar na ki a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya kan ƙudurin neman dakatar da buɗe wuta nan take a yaƙin Gaza.

Kudurin da ƙasashe 10 marar sa kujerar dindindin a kwamitin su ka gabatar, kazalika na buƙatar sake dukkan fursunoni ba sharaɗi da kuma ba da damar shigar da kayan agaji yankin na Gaza wanda Isra’ila ta sha kawowa tarnaki.

Amurka ce kaɗai cikin ƙasashe 5 masu kujerar dindindin a kwamitin da ta hau kujerar na ƙi kuma dama ta saba yin hakan a baya,

Ba mamaki a samu sauyin matsayar Amurka idan an rantsar da sabuwar gwamnatin Donald Trump a badi. Taron kada ƙuri’ar kwamitin tsaron ya ƙarƙare ne da musayar kalamai na rashin samun matsaya ɗaya inda Amurka ke ganin tsagaita wutar ta nan take na nufin Hamas ta cigaba da mulkin Gaza.

Zuwa yanzu fiye da mutum 44,000 ne su ka mutu a Gaza sanadiyyar ruwan boma-bomai da hare-haren kasa na Isra’ila.

Hakanan an kidaya fiye da mutum 130,000 da su ka samu raunuka a Gaza da kuma kasancewar kusan dukkan al’ummar yankin sun rasa muhallin su.

Bayanan na nuna adadin ma wadanda su ka rasa ran su zai fi wanda a ka ambata don za a iya samun wasu gawawwaki a kasan ruguzazzun gine-gine.

Kimanin kashi 70% na wadanda su ka mutu mata ne da kananan yara. An fara yaƙin Gaza tun ranar 7 ga watan Octobar bara kuma duk yunƙurin neman tsaida yaƙin na neman cin tura.

Kammalawa;

Da irin wannan yanayi na kwan gaba kwan baya, sai tsananin rabo ne zai sa nan kusa a tsagaita asarar rayuka a Gaza da Lebanon. Adalcin duniya sau da dama na zama na kashin dankali manya a kan ƙanana. Addu’a na da muhimmanci dare da rana.