Ba a yi zaɓen Shugaban Nijeriya kan tsarin INEC ba – Chatham House

Daga AMINA YUSUF ALI

Chatham House, wata ƙungiya ce mai zaman kanta a kan dokoki wacce take a Landan, ta bayyana cewa, daga nazarin da ta yi na zaɓen shugaban ƙasa ya bayyan cewa har yanzu hukumar zaɓe ta INEC ba ta koyi sababbin darasi ba.

Ƙungiyar wacce Dakta Leena Koni Hoffmann, ta yi rubutun jawabin nan a maimakonta, ta ƙara da cewa, hukumar zaɓen ta kasa bin tsarinta wanda ta tsara da kanta kafin zaɓen, musamman ma da ta ce za ta dinga ɗora sakamakon zaɓe kai-tsaye. 

Ƙungiyar mai zamanta a Landan ta yi misali da alƙalumman Fitch Solutions da suka rage darajar alƙalumman makin Nijeriya zuwa 17.5 daga cikin 100, daga 25.0 da yake a da. A cewar ta, makin ya ragu duba da raunin daraja da ƙasar ta samu sakamakon bayayan Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasa.

A makon da ya gabata ne dai ranar Laraba hukumar zaɓe ta INEC ta ba da sanarwar tsohon gwamnan jihar Legas a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ƙasar. Sai dai kuma Chatam House da wasu ɓangarori a siyasar ƙasar suna jayayya da wannan sakamako. 

Yayin da ɗan takarar shugaban ƙasa na jamiyyar LP,  Mista Peter Obi, ya tunkari kotu don ƙalubalantar sakamakon, shi kuma ɗan takarar jam’iyyar PDP Mista Abubakar Atiku, shi ma ya ba da sanarwar zai je zuwa kotu don ƙalubalantar zaɓen, sannan ya jagoranci zanga-zangar ƙalubalantar sakamakon zaɓen a ranar Litinin. 

Inda Chatam suka bayyana cewa, sakamakon zaɓen tozarci ne ga ‘yancin tsayawa takara da zaɓe na ɗan’adam. Sannan duk da kasancewar Nijeriya wacce ta fi dukka ƙasashen Afirka rajistar zaɓe, inda mutane miliyan 93.4 ne suka yi rajistar zaɓe, amma ba a ƙirga ingantattun ƙuri sun fi miliyan 25 ba a zaɓen, 2023.

Dakta Leena Koni Hoffmann, wacce abokiyar haɗaka ce ta shirin na Chatam a Afirka ta ƙara da cewa, har ma da rashin rarraba kayan zaɓe a kan lokaci wanda ya hana a fara zaɓen da wuri, shi ma ya hana mutane masu rajista da dama yin zaɓen. 

Chatham House, wadda aka kafa tun a shekarar 1920 wacce aka sani ma da ƙungiyar masarauta ta al’amuran ƙasa da ƙasa, kuma tana da shalkwatarta a Landan. 

Ta bayyana babban aikinta da yin sharhi a kan alamuran da ke faruwa a Duniya da kuma kawo maslaha a kan ƙalubalen duniya.