Ba gaskiya ba ne cewa ni ne mamallakin wajen haƙar ma’adinan matasan Neja 37, inji IBB

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon shugaban mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida ya musanta iƙirarin cewa ya mallaka ko yana da hannu a wani gurin haƙar ma’adinai a Jihar Neja, inda aka kama wasu matasa 37 da ake zargin su da yin aikin haƙo ma’adinai ba bisa doka ba da daga bisani suka rasu a komar hukumar Sibil Difens (NSCDC).

Babangida, wanda aka fi sani da IBB, ya bayyana wannan zargin a matsayin ƙarya mara asali da ba shi da makama, kamar yadda wakilinsa, Dakta Ɗanladi Umar Abdulhameed ya bayyana.

Wannan na zuwa ne bayan iƙirarin da wani wanda ya tsira mai suna Malam Babawo Tudun Nasera ya yi na cewa wajen haƙar ma’adinan na tsohon shugaban ƙasar ne. Nasera ya bayyana haka ne a lokacin da yake bayar da ba’asin kamen masu haƙar ma’adinan, ciki har da ɗansa mai suna Salim, wanda daga bisani ya rasu a hannun hukumar kare fararen hular.

Ya bayyana cewa, duk da cewa a baya an hana su aiki a wajen, daga bisani mai wajen ya amince da su cigaba da harkokinsu, inda ya yi ishara ga IBB.

Da yake bayar da amsa game da wannan rahoto, Babangida, ta hannun Abdulhameed ya musanta hannu a aikin haƙo ma’adinan, yana mai cewa zargin ba gaskiya ba ne kuma ba shi da tushe. Ya bayyana cewa, Babangida ba shi da hannun acikin al’amarin don haka ya buƙaci a gyara rahoton tare da kira ga al’umma da su yi watsi da zargin.

By Babaji

Leave a Reply