Ba hurumin Fadar Shugaban Ƙasa ba ne hukunta Sanata Ndume da Ningi – Ministan Labarai

Spread the love


Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Tarayyar Nijeriya ta wanke Fadar Shugaban Ƙasa ko Ɓangaren Zartarwa na Tarayya baki ɗaya tana mai cewa, ba su da hurumin dakatar da Sanata Ali Ndume ko Sanata Abdul Ningi, waɗanda Majalisar Dattawa ta hukunta su a kwanakin baya.
A yayin da ya ke amsa tambayoyi a kafar yaɗa labarai ta BBC a ƙarshen mako, Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan, ya na mai cewa, ko kusa babu hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu a hukunce-hukuncen da Majalisar Dattawa ta yi wa ‘ya’yan nata.
Ya ce, “na farko ka ga shi Sanata Abdul Ningi ai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ne ya dakatar da shi, ‘yan Majalisar Dattawa, inda ya ke aiki, su ne suka ce a dakatar da shi. Shi kuma (dakatar da Sanata Ali Ndume) sun dogara ne da shawarar da aka kawo daga jam’iyya, wato daga Jam’iyyar APC.
“Su ne suka rubuto, a nazarinsu su na ganin a furuce-furucensa yana wuce gona da iri.
“Amma ita Gwamnatin Tarayya, shi Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ka ji ya ce uffan ba akan wannan lamari, (kuma) ba ka ji mu mun yi magana akan wannan abun ba.
“Kenan ka ga matsala ce tasu da abokan aikinsu na Majalisar Dattawa da kuma ita kanta jam’iyya ta APC.
“Eh, mun sani cewa, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da wasu abubuwa, amma dai ba tanka ma sa ba.
“Ka ga misali, idan da babu irin wannan ‘yanci, ai ka ga da sai gwamnati ta ce a kira Ali Ndume a tambaye shi.
“Ba a kira shi ba, saboda ta na ganin idan ma akwai abinda ake ganin ba daidai ba ne, su ‘yan Majalisar Dattawa su ya kamata su duba wannan al’amari su kuma ɗauki matakin da suka ga ya dace.”
Idan za a iya tunawa, a watanni kaɗan baya, majalisar ta dakatar da Sanata Ningi bisa zargin cushe da amfani da kasafin kuɗi biyu da ya yi a kafar yaɗa labarai. Haka nan a makon da ya gabatar majalisar ta sauke Sanata Ndume daga muƙaminsa na Bulaliyar Majalisa bisa zargin da ya yi na cewa, makusantan Shugaba Tinubu su na hanawa a gan shi, don kada a sanar da shi gaskiyar halin da ‘yan ƙasa ke ciki na matsin rayuwa.
Minista Idris ya yi ƙarin da haske cewa, ba al’adar gwamnati Tinubu ba ce ta riƙa tauye haƙƙi ko cin dunduniyar masu faɗin albarkacinsu, ya na mai cewa, gwamnatin ta duƙufa ne wajen gyaran ƙasa da farfaɗo da walwala a rayuwar ‘yan Nijeriya ne kawai.

By ukarofi