Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa, bambancin ta da sauran gwamnatocin baya shine, ta yarda kuma ta amsa cewa, akwai matsaloli da suke addabar al’ummar ‘yan Nijeriya, waɗanda suke buƙatar a gaggauta shawo kansu saɓanin yawancin gwamnati a ƙasar da ba su iya fitowa su amince da cewa, akwai matsalolin.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, a zantawarsa da BBC a ƙarshen makon nan.
Idris, wanda ya ke amsa tambaya kan halin matsin rayuwa da talakawan ƙasar ke ciki, ya ce, “na farko bari na gaya maka cewa, ita gwamnati ta yarda akwai wannan matsatsi. Abinda ya bambanta ita gwamnatin Bola Ahmed Tinubu shine, idan akwai matsala, akan amsa a ce lallai akwai matsala a guri kaza, amma kuma ga abinda muke na a samo maslaha.”
Daga nan sai ya ƙara da cewa, Gwamnatin Tarayya tana taka rawa wajen ganin ta magance matsalolin tsaro da talauci, inda ya bayar da misali da yadda a yanzu hanyar Abuja zuwa Kaduna aka daina samun fargabar yin garkuwa da mutane da kuma yadda Babban Bankin Nijeriya ya fitar da takin zamani buhu miliyan 150, don raba wa manoma ta yadda za a inganta harkokin noma, domin wadata ƙasa da abinci.
