Ba na buƙatar sake zama shugaban jami’a, inji Farfesa Abdallah

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Shugaban (VC) Jami’ar ‘National Open University of Nigeria’ (NOUN) da ke Abuja, Farfesa Abdallah Uba Adamu, ya yi watsi da kiraye-kirayen da ake masa ta kafar Soshiyal Mediya na neman ya karɓi tayin zama sabon shugaban Jami’ar ‘Northwest University, Kano’ ta Jihar Kano, yana mai cewa ba shi da ra’ayin sake karɓar wani muƙamin da ya shafi harkar jagoranci.

A wata takarda da ya fita a yau Asabar, Farfesan ya ce da fari bai samun labarin yaɗa kiran da ake masa ba ta kafar sada zumunta sai a kwanan nan, lamarin da ya sa ya shiga mamaki da nuna rashin gamsuwa da hakan.

Ya bayyana cewa, yayin da yake yabawa da mika godiyarsa ga ƙaramcin da jama’a suka yi masa, haka kuma ba shi da burin sake karɓar wani muƙamin gudanarwa, saboda ko a baya ma ya sha dakatar da yunƙurin neman ba shi irin muƙamin daga wasu jami’o’i.

Farfesa Abdallah ya riƙe muƙamin VC a NOUN daga shekarar 2016 zuwa 2021. A baya ne ya ƙi karɓar tayin irin matsayin daga jami’o’in Kimiyya da Fasaha ta Wudil da Bayero waɗanda dukkanin su a jihar Kano suke.

“Gabanin a naɗa ni VC a NOUN, jami’o’i biyar a lokuta mabanbanta sun buƙaci na nemi muƙamin VC. Na ƙi amsa wa dukkan su. Na ɗauki naɗina na NOUN a matsayin ƙaddara, sannan na karɓe shi.

Kazalika, Abdallah Uba ya ce ya ɗauki matakin barin harkar jagoranci ne don raɗin kansa, inda ya ƙara da cewa yana fara aiki a matsayin VC, ya fara lissafi ranar da zai bar aiki, wanda shi ne 11 ga Fabarairun 2021, lamarin da ya fusata wasu daga cikin jami’an jagorancin makarantar.

Har’ilayau, Farfesan ya ce ya ƙi karɓar aiki daga jami’o’in kuɗi guda biyu bayan ya kammala aiki a NOUN, yana mai jaddada matsayarsa ta ƙin amince wa irin buƙatar a koda wane lokaci.

By Babaji