

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Injiniya Rabiu Aliyu, Shugaban kamfanin Syrol Technologies ya wallafa hakan a shafukansa na sada zumunta a ranar Juma’a inda ya ce, “Wace doka ce ta bai wa ƴan sanda damar yaɗa waɗanda ake zargi da laifi a social media? Mene ne yasa a Jihar Kano da wasu jihohin Arewa ne kaɗai ake daukar video/hoton waɗanda ake zargi da laifi ba tare da hukuncin kotu ba a yaɗa?”
“EFCC suma sukan yaɗa hotunan masu laifi, saidai mafi yawanci bayan masu laifin suke ɗauka domin su ɓoye fuskokinsu da identity nasu. Haka zalika a shawran jihohin ƙasar. Menene yasa mu a Arewa ba haka ba”, inji shi.
Ya kuma ce, “Shamsiyya dai mace ce da ake sa ran za ta yi Aure ta hayayyafa nan gaba, wannan tonon silili da aka yi mata zai bibiye ta da ma ƴaƴan da za ta haifa nan gaba bibiya na har abada.”
Ya ƙara da cewa, “Kowa yana yin laifi, kowa yana da ƙaddararsa a rayuwa. Haka ƙaddarar Shamsiyya tazo, Allah ya kiyaye gaba, Allah ya shirya ta kuma.”
Sannan ya ƙarƙare da cewa, “Yadda masana doka da ƴan jaridu na Jihar ta Kano suke ta yaɗa wannan yarinya a maimakon su soki lamarin tunda dokar ƙasa da addinin Musulunci da al’adar Hausa ba sa goyan bayan yaɗa hotununan masu laifi ta wannan sigar.
“Shamsiyya ta yi laifi, ya kamata a gurfanar da ita a kotu a yanke mata hukunci kamar yadda ake wa ragowar masu laifi a ko’ina a faɗin Najeriya, wanda na san hukumar ƴan sandan jihar za su yi hakan koma ƙila sun yi tuni amma, yaɗa waɗanda ake zargi da laifi ko da ma ba mace ba Ina ga ya saɓa da koyarwar addinin Musulunci da al’adar Hausa haka zalika a dokance,” inji Injiniya Aliyu.
