



Daga BELLO A. BABAJI
Gwamna Bala Abdulƙadir Mohammed na jihar Bauchi, ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa ba za ta tsoma baki cikin ayyukan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Bauchi (BAROTA) da aka kafa ba, yana mai jaddada buƙatar yin gaskiya da nuna sanin makamar aiki a hukumar.
Da ya ke jawabi a bikin ƙaddamar da rukunin farko na kadet na jami’an BAROTA 500 da Marshal a filin wasa na Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu da ke gidan gwamnatin Bauchi, gwamnan ya bayyana cewa an samar da BAROTA ne domin magance matsalolin da suka addabi sha’anin zirga-zirgar ababen hawa, tsaro, tare da tilasta bin dokokin ababen hawa da dai sauransu a jihar.
Ya ce ayyukan BAROTA sun haɗa da tabbatar da dokokin zirga-zirga, hana haɗurra, wayar da kan jama’a kan hanyoyin kiyaye haɗurra, da kuma binciken musabbin haɗurra na ababen hawa.
Kazalika, dokar ta bai wa jami’an hukumar ikon kama masu laifi, ɗaure ababen hawan da ke da hannu wajen keta waɗannan dokoki, tare da tabbatar da yin amfani da hanyoyin cikin tsari da doka.
