Yan Sanda a Katsina sun kuɓutar da mutane 18 daga hannun ‘yan bindiga

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

‘Yan sanda a Katsina sun sami nasarar kuɓutar da mutane 18 da suka fito daga ƙaramar hukumar Batsari za su garin Yankara da ke ƙaramar hukumar Faskari.

‘Yan bindigan sun tare motocin hayar guda huɗu ɗauke da waɗannan mutane a hanyar Funtua zuwa Gusau.

Jami’in yaɗa labarai na rundunar ‘yan sanda a Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya shaidawa manema labarai haka a Katsina.

Ya faɗa cewa motocin haya ɗauke da waɗannan mutane akan hanyar su na zuwa Yankara su kai karo da ‘yan bindiga a babban hanyar Funtua zuwa Gusau.

Ko da samun rahoton haka babban jami’in ɗan sanda na ƙaramar hukumar Faskari da mutanen sa su ka kaiwa mutanen ɗauki, a cewar ASP Sadiq.

Ya bayyana cewa bayan tafka gumurzun faɗa da ƴan bindigan,ƴan sandan yankin sun sami nasarar kuɓutar da mutanen 18 ba tare da wani ya sami rauni ba.

Haka kuma kuma ƴan sanda sun fatattaki ƴan bindiga a ƙauyen Fanisau da ke ƙaramar hukumar Ƙafur bayan samun rahoton hare hare da ƴan bindigan su ka kai wa ƙauyen.

Haɗin gwiwa na ƴan sandan Malumfashi da Ƙafur suka kai wa ƙauyen ɗauki,sai da babban jami’in ƴan sanda mai kula da Ofishin ƙaramar hukumar Malumfashi shi kaɗai ya sami rauni kuma yana samun kulawa a asibiti.

Kwamishinan ‘yan sanda a Jihar Katsina CP Aliyu Abubakar Musa ya jinjina wa jami’an sa bisa ƙwazo da ƙwarewa da suka nuna wajen ceto mutanen da ƴan bindigan sukai ƙoƙarin sacewa.

Ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa ƴan sanda za su ƙara himma wajen tabbatar da tsaro a jihar.

By ukarofi