Gwamnatin Katsina za ta ɗauki ma’aikata 70 da za su kula da dazuka

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya bada umarnin ɗaukan ma’aikata guda saba’in da za su kula da dazukan da ke jihar.

Wannan mataki da gwamnati ta ɗauka ya biyo bayan rahoton da ya samu na cin iyaka da saran itace ba bisa ƙa’ida ba a dazuka na gwamnati tun shekara 2017 zuwa yanzu.

Gwamna Raɗɗa ya ce ayyukan ma’aikatan dajin shine kula da sa ido kan masu saran itace ba bisa ƙa’ida ba da musu cin iyaka a dazukan, sanarwar ta ce.

Gwamna Dikko Raɗɗa ya amince wa ma’aikatar aikin gona ta kula da aikace-aikacen ma’aikatan dajin.

Ya kuma sanar da kafa kotuna na musamman da za su hukunta masu cin iyaka da sare itace a dazuka.

A cewar Gwamna Raɗɗa, gwamnati ta ɗauki wannan mataki domin kare dazukan da albarkatun ƙasa da Allah ya wadata jihar da su.

By ukarofi