Ba na shakkar EFCC, inji Gwamnan Zamfara

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin ƙasa Zagon ƙasa ta EFCC ba ta ba shi tsoro ba, yana mai jaddada cewa ya kamata jami’an gwamnati su rungumi riƙon amana da kuma nuna gaskiya a cikin ayyukansu.

Da yake jawabi a ranar Talata a wurin taron ƙasa da ƙasa kan ayyukan damfara ta intanet, wanda hukumar EFCC tare da haɗin gwiwar hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Tarayyar Turai ta shirya, na Cibiyar Dimokraɗiyya da Taimakon Zaɓe ta Duniya (International IDEA), Lawal ya jaddada ƙudirinsa na samar da shugabanci na gari.

“Bana tsoron EFCC. Me ya sa zan ji tsoro? Muna nan muna yi wa al’umma hidima, kuma wannan ita ce kaɗai burin mu. Ya kamata shugabanni su kasance masu riƙon amana ba riƙon sakainar kashi ga shugabanci ba, wannan shi ne ainihin shugabanci,” inji Lawal.

Gwamnan ya kuma yi jawabi a wata ƙara da aka ce wasu takwarorinsa gwamnonin ne suka shigar a kan hukumar ta EFCC, inda ya bayyana cewa bai san matakin da doka ta ɗauka ba amma ya jaddada goyon bayansa ga ƙoƙarin hukumar.

“Ina jin labarin wannan ƙarar a karon farko, kuma ba zan iya yin tsokaci kan wani abu da ban sani ba. Sai dai kasancewata a yau ya nuna goyon bayana ga hukumar EFCC, musamman a daidai lokacin da Nijeriya ke fuskantar ƙalubale masu nasaba da aikata laifuka ta intanet,” inji shi.

Lawal ya jaddada muhimmancin yin aiki tare don dawo da martabar Nijeriya a idon duniya. “Wannan wata dama ce ta magance laifukan yanar gizo, kuma dole ne mu yi amfani da shi don kwato martabar Nijeriya a cikin ƙasashen duniya. A matsayina na gwamna, na ƙuduri aniyar tallafawa ƙoƙarin da ake na kawar da aikata laifuka ta yanar gizo,” inji shi.

Shi ma shugaban shirin na IDEA na ƙasa da ƙasa, Danladi Plang, ya yi jawabi a wajen taron, inda ya bayyana yadda ake samun ƙaruwar aikata laifuka ta yanar gizo, sakamakon ƙaruwar fasaha. Ya yi nuni da cewa matasan Nijeriya, waɗanda suka kware a fasahar zamani, a wasu lokuta suna amfani da waɗannan fasahohi wajen aikata laifuka, kamar zamba ta kuɗi da yaɗa bidiyon batsa ga ƙananan yara.

Yayin da yake yaba wa ƙoƙarin hukumar EFCC da sauran jami’an tsaro na yaƙi da ta’addanci ta yanar gizo, Plang ya buƙaci a sauya dabarun. “Muna buƙatar mu sake tunanin tsarin wajen kama masu laifi, da bin hanyar shari’a wajen yanke musu hukunci,” inji shi.

By ukarofi