Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
An bayyana cewa naɗa Hakimin Warawa, ɗan Isan Kano Alhaji Kabiru Tijjani Hashim, sabon Turakin Kano ya dace, saboda yadda ya ke taimakawa al’umma musamman talakawansa na Warawa, da sauran su a matsayinsa na tsohon ɗan Isan Kano hakimin warawa sabon Turakin Kano na yanzu domin kakansa ya yi mahaifinsa ya yi wannan sarauta da ta yi suna wajen kwarjini da kuma taimakawa al’ummar Kano da wajenta, kamar dai yadda Malam Rabiu Zubairu Sakataren Hakimin Warawa kuma Dagacin Kanta ya bayyana bayan naɗa sabon ɗan Isan Kano Hakimin Warawan da mai martaba Sarkin Kano Malam Sunusi na II ya yi a ranar Juma’a da ta gabata.
Dagacin Kanta wanda ya yi magana a madadin Dagatan Warawa 28 da masu unguwan ni 218 na Warawa ya ce shirye su ke su ba wa Turakin Kano haɗin kai kamar yadda su ka ba shi a baya yana ɗan Isan Kano, domin shi dai yasan tun da aka naɗa shi Hakimin Warawa tun watan 11 na 2014 da ya fara aiki ba a taɓa samun wata matsala da shi da talakawan Warawa ba. Haka ma idan wasu abubuwan na sun taso da kansa ya ke taimakawa talakawa kamar ta fannin lafiya, ilimi, da sauransu, ya ce akwai lokacin da wata rijiya da ta ke haddasa cututtuka ga talakawan yankin a wani ƙauye a Warawa da kan sa ya je ya ɗauki mataki a ka dai na samun matsala a wannan rijiya sai kuma tallafi na wutar lantarki da matsalar ruwan sha da ya warware a makarantar almajirai ta zamani da ake kira Almajiri Modern School, da dai saurinsu, shi mutum ne mai son gaskiya da adalci babu nuƙu-nuƙu a tafiyarsa a cewar Malam Rabiu Zubairu, Dagacin Kanta Malamin Hakimin Warawa Turakin Kano.
Hajiya Sakina Ali Hashim ta ce mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi ya riƙe alƙawari ya karramasu kuma ɗaukacin iyalai da masoyan Marigayi Galadimman Kano Alhaji Tijjani Hashim na farin ciki da addu’a ga al’ummar Kano da Nijeriya kan ƙaunar da ake nuna musu a da da yanzu.
