Ba zan bayyana komai ba kan sulhun zaman lafiya da Fubara – Wike

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa ba zai bayyana cikakken bayani kan sulhun da aka yi tsakaninsa da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ba, inda ya ce abu mafi muhimmanci shi ne zaman lafiya ya dawo a jihar.

Wike ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake tattaunawa da manema labarai a gidansa da ke Abuja. Ya ce maimakon bayyana cikakken bayani game da yarjejeniyar zaman lafiyar, maimakon haka zai bar mutane su yi hasashe.

“Zan ba ku damar yin hasashe, ba aikina ba ne. Abin da na sani shi ne zaman lafiya ya samu,” inji Wike.

“Idan ba ku gamsu da hakan ba, babu abin da za mu iya yi, abin da ke da muhimmanci shi ne zaman lafiya ya dawo, duk abin da wani ya ce ba daga ni ba ne.”

Ya bayyana cewa wasu mutane sun mayar da rikicin jihar Ribas wata sana’a mai riba, inda suke amfani da shi wajen arzuta kansu ba bisa ƙa’ida ba don son kai.

Ya ƙara da cewa yanzu waɗannan mutane ba su ji daɗin sulhuntawar da ya yi da gwamnan jihar da aka dakatar, Siminalayi Fubara ba.

A watan da ya gabata ne Tinubu ya shirya taron sasantawa tsakanin Wike, Fubara da ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas da aka dakatar, lamarin da ke nuni da dawowar zaman lafiya a jihar.

Shugaban ƙasar ya dakatar da Fubara, da mataimakinsa, Ngozi Odu, da kuma ‘yan majalisar Ribas a watan Maris din shekarar 2025, bayan dambarwar siyasa da aka daɗe ana yi a jihar mai arzikin man fetur.

An samu takun saƙa tsakanin Wike da Fubara, dan ubangidansa na siyasa, kan kula da gine-gine a jihar. Lamarin ya taɓarɓare yayin da ‘yan majalisar da ke biyayya ga Ministan Babban Birnin Tarayya – ƙarƙashin jagorancin Martin Amaewhule – suka yi yunƙurin tsige Fubara.

Ba tare da ɓata lokaci ba, Tinubu ya dakatar da ‘yan majalisar, Fubara da mataimakinsa, sun naɗa tare da rantsar da wani hafsan sojan ruwa, Vice Admiral Ibok-ete Ibas mai ritaya, a matsayin mai kula da jihar shi kaɗai.

By ukarofi