Cibiyar Taro Ta Tinubu ta samar da miliyan N650 a mako uku, inji Wike

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya yi ikirarin cewa cibiyar taron ƙasa da ƙasa ta Bola Tinubu ta samar da Naira Miliyan 650 makonni uku da ƙaddamar da ita.

Wike ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 3 ga Yuli, 2025.

Ya ce, kafin a gyara cibiyar taron, babban birnin tarayya Abuja na samun kuɗaɗen shiga na Naira Miliyan 50 ne kacal a duk shekara.

“Yanzu bari in gaya muku yadda ƙasar nan take aiki, mutumin da aka sakar wa riƙon cibiyar taron a da yana biyan Naira miliyan 50 ga babban birnin tarayya Abuja duk shekara, an ba da wannan wurin ne a ranar 10 ga watan Yuni, kuma kuɗaɗen shiga da aka samu a cikin makonni uku ya kai Naira miliyan 650, me ya sa mutane ke son abu mai kyau,” inji shi.

“Shugaban ya karɓi baƙuncin shugabannin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) a cibiyar taron ƙasa da ƙasa, ku je ku ga jawaban jakadun, jama’a na ta tururuwa zuwa neman hayar wurin a yanzu.

“A gaskiya, babu sarari. Kamar yadda nake magana, an yi rajista har zuwa 2027.”

Wike ya ce, da farko da ya rufe cibiyar, ya samu tsokaci da dama daga ‘yan siyasa da manyan jami’an gwamnati.

“ƙasar da muke ciki wuri ne da idan kun fara mai da hankali kan rashin gaskiya, ba za ku cimma komai ba,” inji shi.

“Kuma yanzu kuna cewa, me ya sa na sanya wa Tinubu suna, wa zan sa masa suna? Wa ya fi cancanta?”

Hukumar Birnin Abuja ta fuskanci suka kan kashe Naira Biliyan 39 don inganta cibiyar taron.

An kuma soki Wike da sanya wa ginin da aka gyara sunan shugaban ƙasar.

By ukarofi