Dalilan da suka sa yajin aikin malaman makarantun firamare da sakandare ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a Abuja – NUT

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Malaman makarantun firamare da sakandaren gwamnati a Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja sun yi watanni huɗu kenan suna yajin aiki.

ƙungiyar Malamai ta ƙasa reshen Abuja ta ce abin takaicin shine yadda ƙungiyar a tsakanin wannan lokaci ta riƙa kai ruwa rana domin ganin gwamnati ta biya buƙatunsu amma har yanzu shuru ba ta ce komai ba.

Daga cikin buƙatun nasu akwai biyan malamai da sabuwar amintacciyar tsarin mafi ƙarancin albashi, biyan su alawus ɗin su, ƙara wa malaman girma na tsawon shekarun da suka gabata da dai sauransu.

Manhaja ta yi ƙoƙarin tattaunawa da mataimakiyar shugaban fannin yaɗa labarai na ofishin Ministan Abuja Rabi Umar, Kabir Musa kakakin hukumar Kula da Ilimin boko ta FCT da shugaban hukumar Kula da ayyukan ƙananan hukumomi ALGON Chiya ɗanladi amma duk ba su ce komai ba game da batun.

Sakataren hukumar Kula da Ilimin Boko UBEC na FCT Alhassan Sule ne kaɗai ya amince ya tattauna da Manhaja inda yake cewa Hukumar Ilimi ta FCT za ta haɗa hannu da hukumar Kula da Ayyukkan ƙananan hukumomi da ƙungiyar NUT domin kawo ƙarshen yajin aikin.

Sule ya ce ya tattauna da shugaban hukumar kula da gundumomin Abuja inda yake tabbatar masa da cewa basu da kuɗin da za su iya biyan albashin malamai da sabuwar tsarin mafi ƙarancin albashi ba.

Ya ce shugaban hukumar ya ce suna sa ran malaman za su yi haƙuri da gwamnatin Abuja su janye yajin aikin domin gwamnati ta samu damar tsara matakan da suka fi dacewa don cimma burinsu.

Ga dalilan da ya sa malamai ke yajin aiki a Abuja.

Nuna wa malamai wariya da rashin cika alƙawari da buƙatun malaman. Muhammed ya ce buƙatun malaman sun haɗa da biyan su da Naira 70,000 sabon tsarin mafi ƙarancin albashi, yi musu ƙarin kashi 40 a alawus ɗinsu, biyan su sauran alawus ɗinsu tare da yi musu ƙarin girma da ya kamata a yi a shekarun da suka gabata.

Yawan kai ruwa rana tsakanin ƙungiyar NUT da gwamnati ba tare da ya haifar musu ɗa mai ido ba; Yin sama da faɗi da Naira biliyan 4.1 da ƙungiyar shugabanin gundumomin Abuja suka yi. Sai kuma rashin ɗaukan mataki da Ministan Abuja ya ƙasa yi.

By ukarofi