Kada ku bari dukiya ta raba kawunanku – Shettima ga iyalan Ɗantata

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya yi kira ga iyalan marigayi kuma hamshaƙin attajiri, Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata da su cigaba da kasancewa masu haɗin kai da koyi da kyawawan halayensa na tausayi da taimakon al’umma.

A lokacin da ya ke magana yayin ta’aziyya ga iyalan marigayin a Kano a madadin Shugaba Bola Tinubu, Shettima ya bayyana mamacin a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan Nijeriya, wanda rashin sa ba iya iyalan nasa ya shafa ba har ma ƙasar baki ɗaya.

Ya ce, rayuwar Ɗantata cike ta ke da albarka ga al’umma da Nijeriya a matsayinta na ƙasa, yana mai kira ga iyalansa da kada su bari dukiya ta raba kawunansu.

“Mai dukiyar ya tafi. Wannan ya isa tunatar da mu cewa a wannan duniyar babu abinda ya ke dawwama”, inji Shettima.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma buƙaci iyalan da su cigaba da kiyaye kima da darajar marigayin wajen riƙe gaskiya, kyautayi da ƙoƙarin samar da ci-gaba acikin al’umma.

Shettima ya je Kano ne domin isar da saƙon ta’aziyar Gwamnatin Tarayya bisa rasuwar Ɗantata, wanda ya rasu a Abu Dhabi bayan shafe shekaru 94 a duniya, inda aka yi jana’izarsa a Madina.

By Babaji