
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, GCON, ya ƙaddamar da sabon tsarin Hukumar Daraktoci ta Kamfanin Tabbatar da Lamuni na Ƙasa (NCGC) a yayin wani muhimmin zama da aka gudanar a birnin tarayya Abuja, ranar Alhamis.
An kaddamar da hukumar ne a ƙarƙashin jagorancin Rt. Hon. Yakubu Dogara, tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ta Ƙasa.
Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin tarayya na inganta damar samun lamuni da tallafa wa ƙananan ƴan kasuwa da masana’antu, ta hanyar samar da tabbacin lamuni don bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya bayyana muhimmancin NCGC a matsayin ginshiƙin da zai taimaka wajen haɓaka harkokin kasuwanci da samar da ayyukan yi ga ƴan Najeriya, musamman matasa da mata.




