Babban jami’in Africa CDC ya jinjina wa ƙasar Sin bisa haɗin gwiwarta a fannin sarrafa rigakafin COVID-19 a Afirka

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Muƙaddashin daraktan cibiyar kandagarki da yaƙi da annobar COVID-19 ta Afirka, ko Africa CDC Ahmed Ogwell Ouma, ya jinjinawa ƙasar Sin, bisa shiga haɗin gwiwar sarrafa alluran rigakafin cutar COVID-19 da ta yi tare da wasu ƙasashen Afirka.

Mr. Ouma, ya ce haɗin gwiwar Sin da ƙasashe irin su Masar, da Algeria, da Morocco, ya samar da ƙarin dama ta sarrafa rigakafin COVID-19 a cikin nahiyar, musamman a gabar da aka samu yawaitar bazuwar cutar a tsakiyar shekarar 2021 da ta gabata.

Jami’in ya ƙara da cewa, haɗin gwiwar sassan ya bai wa Afirka damar sarrafa rigakafi a cikin nahiyar, matakin da ya rage buƙatar safarar sa daga wajen nahiyar.

Kazalika, ya jinjinawa Sin bisa yadda ta rika samarwa Afirka rigakafin kyauta, tun lokacin da aka fara yiwa al’umma alluran.
Mr. Ouma, wanda ya yi wannan tsokaci a gefen bikin ƙaddamar da shirin kare rayuka, da walwalar al’ummar kudancin Afirka, wanda Afirka CDC da hadin gwiwar gidauniyar Mastercard suka shirya, ya ce an ƙaddamar da shirin ne domin haɗe sassan ƙasashen kudancin Afirka 10, da nufin ƙarfafa musu gwiwar cimma nasarar yiwa al’ummun su rigakafi.

Daga nan sai ya bayyana shirin da ake yi, na ƙaddamar da makamancin shirin a ƙarin sassan nahiyar 4, ta yadda za a kai ga yiwa kusan kaso 70 bisa dari na al’ummun Afirka, wadanda suka cancanci karɓar rigakafin su kimanin biliyan 1.3 alluran, nan da ƙarshen shekarar nan ta 2022.

Mai fassara: Saminu Alhassan

By Editor