Rahoto da yake isa jaridar Blueprint ya nuna cewa wata babbar kasuwa a Karu ta kama da wuta.
Ƙwararren ɗan jaridan nan, Ezeocha Eze ne ya sanar ta manhajar WhatsApp a daren Alhamis.
Yace masu yaƙi da gobar sun hallara domin kashe gobarar amma duk da haka wutar na cigaba da ci.
Har ya zuwa lokacin wallafa rahoton, hukumomi ba suyi magana ba.