Babbar Kotun Tarayya ta tafi hutu

Daga WAKILINMU

A Litinin da ta gabata Babbar Kotun Tarayyar Nijeriya ta soma hutunta na shekara-shekara da ta saba tafiya.

Cikin wata sanarwa wadda Babban Rajistaran kotun, Mr Emmanuel Gakko ya sanya wa hannu, hutun kotun zai ƙare ne a ranar 17 ga Satumba, sannan ta soma aiki ran 20 ga Satumba.

A cewar Gakko, wasu kotuna a yankin Abuja da Legas da Fatakwal za su ci gaba da aiki domin sauraren ƙararrakin gaggawa a yayin da Babbar Kotun ke shan hutunta.

Ya ƙara da cewa, duk masu buƙatar shigar da ƙara na iya yin hakan ta hanyar ziyartar kotu mafi kusa da su a yankunan da kotunan za su kasance a bakin aiki.