Majalisar Dokokin Kano ta buƙaci Ganduje ya sauke Muhyi

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Majalisar Dokokin jihar Kano, ta buƙaci Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da ya sauke dakataccen shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafi da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhyi Magaji Rimin Gado.

Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna majalisar ta buƙaci gwamnan ya ɗauki matakin ne bayan da kwamitinta na wucin-gadi da ta ɗora wa aikin gudanar da bincike kan ƙorafin da ofishin babban akantan jihar Kano ya shigar gaban Majalisar a kwanakin baya.

Kazalika, ta ce yayin zaman Majalisar na yau Litinin, kwamitin ya gabatar wa Majalisar rahotonsa inda a ciki ya nuna Muhyi Magaji ya gabatar musu da rahoton asibitin ƙasa da ke Abuja da ya nuna cewa ba shi da lafiya amma, da kwamitin ya tuntuɓi asibitin sai ya tabbatar da cewa rahoton na boge ne.

Rahotan ya ƙara da cewa, akan gabatar da rahoton ne majalisar ta fitar da wasu shawarwari da za ta aike wa gwamnan, duk da cewa tun a makon jiya wata Babbar Kotun Tarayya ta umarci Majalisar da kwamitin wucin-gadin da sauran waɗanda ake ƙara da kowa ya dakata dangane da batun har sai an je gaban kotun.