Bidiyo: Mamakon ruwan sama ya haifar da ambaliya a Keffi

Daga BASHIR ISAH

Sakamakon mamakon ruwan saman da aka samu a garin Keffi, jihar Nasarawa, hakan ya haifar da ambaliya a wasu sassan garin.

Ruwan saman wanda aka soma da asubahin yau Litinin, an shafe sama da sa’o’i biyar ana tafkawa.

Daga cikin wuraren da aka samu aukuwar ambaliyar har da fitacciyar gadar nan ta Antau, wadda ta cika ta batse da ruwa ta yadda ma amfani da ita ya gagari jama’a.

Bayanan da Manhaja ta tattaro sun nuna ambaliyar Gadar Antau ta shafi wasu gidaje da ke yankin tare da lalata kayayyaki da dama amma ba a samu hasarar rai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *