Babu auren jinsi: Dokokin Nijeriya sun fi ƙarfin Yarjejeniyar Samoa, inji Ministan Labarai

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Gwamnatin tarayya ta bayyana matsayarta game da batun yarjejeniyar ƙasar Samoa inda ta ce dokokin Nijeriya kan auren jinsi sun fi ƙarfin a tanƙwara su.

Yarjejeniyar, ta ƙunshi dokar sanya ƙasashen da ba su ci gaba ba da masu tasowa su amince da auren jinsi (LGBT), wanda yin hakan shi zai bada lasisin samun agajin kuɗi da wasu nau’uka na taimako daga ƙasashen da su ka ci gaba.

Takardar yarjejeniyar Samoa ta na samun karɓuwa a wasu ƙasashe, sai dai ƙasashe da dama sun ƙi amincewa da ita kasancewar auren jinsi abu ne da ya ci karo da al’adun addinan musulunci da na kiristanci waɗanda su al’umma ke yi a cikin su.

Haka nan, batun ya janyo cecekuce a cikin al’umma inda malamai da wakilan kare haƙƙin ɗan-Adam ke sukan gwamnati game da shi.

Sai dai wata sanarwa da mai taimaka wa shugaba Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Mohammed Idris ya fitar a ranar Alhamis, ta yi gamsashshen bayani game da al’amarin.

A ciki, ta yi bayanin cewa, a ranar 24 ga watan Yuni 2024, Nijeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar Samoa a taron haɗaka na ƙasashen Afirka da na Caribbean da kuma na Pacific (OACPS) a sakatariyarsu da ke Brussels a ƙasar Baljika.

Ta kuma ce tattaunawar ta samo asali ne a shekarar 2018 inda a ka sanya ta ciki abubuwan tattaunawa a zaman majalisar ɗinkin duniya na 73 wanda ƙasashe 27 na Tarayyar Turai da kuma 47 cikin 79 na OACPS suka tabbatar da yarjejeniyar a birnin Apia na ƙasar Samoa.

Sannan, takardar ta ƙunshi saɗarori guda 103 wanda akwai yarjejeniyar haɗakar nahiyoyi kan batutuwan da suka shafi kowace nahiya waɗanda galibi kan harkokin ci gaba ne.

Sai dai, yayin sanya hannu a ranar 26 ga watan Yuni, 2024 Nijeriya ta ce duk wata doka da ta ci karo da dokokin kundin tsarin mulkinta, ba za ta amince da shi ba, wanda akwai batun yaƙi da auren jinsi a dokar majalisar zartarwa da aka samar a 2014.

By Babaji