Kenya za ta ƙara ciyo bashi  bayan janye dokar ƙarin haraji – Shugaban Ƙasa

Spread the love

Shugaban Ƙasar Kenya William Ruto ya ce, ƙasar za ta ƙara rance don ci gaba da tafiyar da gwamnatin ƙasar biyo bayan ƙin amincewa da sabuwar dokar ƙarin kuɗin haraji da ake fata ya zama hanyar ƙarin kuɗin shiga ga gwamnatin. 

Shugaban ya ce, zai janye ƙudirin dokar da ke ƙunshe da ƙarin harajin da ya janyo mummunar zanga-zanga a ranar Larabar da ta gabata, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane, inda aka ƙona majalisar dokokin ƙasar.

Sai dai a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana cewa, watsi da ƙudirin ya mayar da ƙasar baya har na tsayin shekaru biyu, kafin ya bayyana illar rashin ƙarin kuɗin shiga ga ƙasar bayan tulin bashin da ke kanta.

A cewarsa, hakan na nufin Kenya za ta ciyo bashin Tiriliyan ɗaya ($7.6bn; £6.1bn) “domin samun damar tafiyar da gwamnatinmu.”

Wannan ƙarin kashi 67% ne akan abin da aka tsara.

Sai dai kuma ya ce, yana tunanin rage kuɗaɗen da ake kashewa a faɗin gwamnati, ciki har da na ofishinsa, da kuma rage kason kuɗaɗen da ake bai wa ɓangaren shari’a da kuma gwamnatocin ƙananan hukumomi.

Masu zanga- zangar da dama dai sun nuna adawa da ƙarin harajin inda suka ce ƙarin kuɗaɗen ba shi da wani tasiri a gudanar da ƙasa.

Ƙarin harajin zai ƙara kusan shilling na Kenya biliyan 350, yayin da za a ci bashi kusan biliyan 600.

A cewar shugaban, matakan harajin da aka gabatar wani ɓangare ne na ƙoƙarin rage bashin da ya haura dala biliyan 80. Kusan kashi 60 cikin 100 na kuɗaɗen shiga na Kenya suna zuwa ne don biyan bashi.

“Na yi aiki tuƙuru don na fitar da Kenya daga tarkon bashi… Yana da sauƙi a gare mu, a matsayinmu na ƙasa, mu ce: ‘Bari mu yi watsi da lissafin kuɗi. Hakan mai yiwa ne.

Kuma na ce na yarda za mu yi watsi da ƙudirin dokar ƙarin kuɗin haraji, amma sakamako da zai haifar ba mai kyau ba ne,” inji shugaban yayin da yake magana da manema labarai a daren Lahadi.

Mista Ruto ya ce, ƙin amincewa da kasafin kuɗin zai shafi ɗaukar ma’aikatan ƙananan makarantun sakandare 46,000 da suka kasance kan kwangiloli na wucin gadi, da kuma samar da kiwon lafiya.

Ya ƙara da cewa, gwamnati ba za ta iya tallafa wa manoman rake da kofi, da kiwo ba, gami da biyan basussukan da masana’antunsu da ƙungiyoyin haɗin gwiwa suke bi kamar yadda aka tsara.

Sai dai ya ce, yana nazarin batutuwan da masu adawa da ƙudirin dokar suka taso, kamar rage kashe kuɗaɗen da ofishinsa ke kashewa da kuma soke kasafin kuɗin uwargidan shugaban ƙasa da kuma uwargidan mataimakin shugaban ƙasa.

Kalaman na baya- bayan nan na shugaban ƙasar game da ƙarin rance sun fuskanci suka, inda masanin tattalin arziki Bo Ramogi ya shaida wa BBC cewa, bai zama dole ko kuma a hankali a ƙara rance ba domin hakan zai sanya Kenya cikin “matsalar bashi.”

Ya ce, furucin da shugaban ƙasar ya yi kan rage kashe kuɗaɗe ba shi da wani tasiri domin ya rattaba hannu kan tsare-tsaren kashe kuɗaɗe a makon da ya gabata.

By ukarofi