Badaƙalar N1.3trn: Har yanzu muna binciken Okowa duk da ya koma APC, inji EFCC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta bayyana cewa tsohon Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, yana cigaba da fuskantar bincike akan zargin badaƙalar kuɗaɗe, duk da cewa ya koma jam’iyya mai mulki ta APC a kwanan nan.

EFCC ta faɗi hakan ne a wata sanarwa, inda ta ce canja jam’iyya ba zai zama kariya daga binciken gaskiya ba, musamman idan akwai shaida da ke nuna yiwuwar aikata laifi a yayin da mutum ke rike da muƙamin gwamnati.

Hakan na zuwa ne bayan da tsohon gwamnan ya sanar da komawarsa APC, lamarin da ya haifar da cece-kuce daga masu ganin cewa hakan wata dabara ce ta guje wa hukunci ko bincike a yayin da aka samu aikata laifi.

Hukumar ta tabbatar da cewa binciken kuɗaɗen jihar Delta a lokacin mulkin Okowa yana cigabada gudanan.

Haka kuma za a kammala shi bisa dokar kasa da hujjojin da ke hannun hukumar ta EFCC’n.

By Babaji