
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wata Kotun Shari’a da ke zaune a Kuje, Birnin Tarayya Abuja, ta bada belin mawallafi kuma ɗan gwagwarmaya, wato Omoyele Sowore da Aloy Ejimkor, wanda ɗaya ne daga cikin lauyoyin da suka wakilci Nnamdi Kanu a kotu da ɗan uwan Kanun, Frins Emmanuel Kanu da wasu mutane goma.
A yau Juma’a ne Kotun ta umarci a sako baki ɗaya mutanen su 13 bisa sharaɗin belin kowannensu akan kuɗi N500,000 da mutum biyu-biyu a matsayin waɗanda za su tsaya musu.
An kama su tare da gurfanar da su ne bisa laifin tayar da hankalin al’umma a yayin zanga-zangar neman sako Nnamdi Kanu, wato tsararren jagoran ƴan fafutukar kafa ƙasar Biafara (IPOB), wadda aka gudanar a ranar 20 ga watan nan na Oktoba.
Rahotanni sun bayyana cewa, an kama Ejimkor, Emmanuel da wasu mutane goma ne yayin gangamin, inda aka tsare su a kurkukun Kuje.
Daga bisani a jiya Alhamis, aka cika hannu da Sowore a farfajiyar Babbar Kotun Tarayya a lokacin da ya halarci shari’ar Nnamdi Kanu domin nuna goyon bayansa a gare shi.
Kama ɗan gwagwarmayar ya haifar da cecekuce acikin al’umma har da masu faɗa a ji ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
