’Yan sanda da tarukan siyasa

Spread the love

A makonnin baya-bayan nan, wata babbar kotu a Jihar Kaduna ta yanke hukunci mai muhimmanci, inda ta bayyana cewa matakin ‘yan sanda na dakatar da taruka da harkokin siyasa a jihar, ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki, kuma babbar ɓarna ce ta amfani da iko fiye da kima.

Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Murtala Zubairu, ta yanke hukunci a kan ƙarar da kwamishinan ‘yan sanda ya shigar kan jam’iyyun ADC da SDP, inda ta umarci ‘yan sandan su biya jam’iyyun naira miliyan 15 saboda tauye musu haƙƙin ɗan Adam.

Mai Shari’a Zubairu ya bayyana cewa, “Tunanin cewa ‘yan sanda za su iya dakatar da haƙƙin taro da haɗin kai na jam’iyyun siyasa gaba ɗaya a cikin wata jiha abu ne da ya wuce iyaka, kuma cin zarafi ne na doka.”

Mu tuna cewa wannan ƙara ta samo asali ne daga rikicin da ya faru lokacin da wasu da ake zargi da ‘yan daba ne suka tarwatsa wani taron siyasa da jam’iyyun SDP da ADC suka shirya a Kaduna, wanda tsohon gwamna Nasir El-Rufai da wasu jiga-jigan ADC suka halarta.

Bidiyon lamarin ya nuna yadda jami’an ‘yan sanda da aka tura don tsaro suka tsaya suna kallo yayin da matasa ke lalata motoci da raunata mahalarta taron, abin da ya haifar da tambayoyi kan rawar da ‘yan sanda suka taka.

A zahiri, rashin ɗaukar mataki daga ɓangaren ‘yan sanda a lokacin wannan tashin hankali ya nuna gazawa wajen cika babban nauyin da doka ta ɗora musu — kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Daga baya, abin mamaki, rundunar ‘yan sanda ta kai ƙara kotu tana neman ta hana gudanar da tarukan siyasa a jihar, wai har sai sun kammala bincike kan barazanar tashin hankali — wani mataki da ya nuna ƙoƙarin kauce wa gaskiya da wajibin aikinsu.

A fahimtarmu, wannan lamari ya sake jefa ‘yan sanda cikin hasashen nuna son kai a siyasa, musamman ganin yadda aka yi gum lokacin da abin ya shafi jam’iyyun hamayya, amma da alama da wani taro ne na jam’iyyar mai mulki, abin ba zai gudana haka ba.

A ƙasar da ake mulkin dimokuraɗiyya, irin wannan yunƙuri na neman daƙile haƙƙin taro da bayyana ra’ayi ya nuna koma baya. Ko da ‘yan sanda sun yi kuskure ne ko kuma suna bin umarni ne marasa dacewa, abin da ya faru abin damuwa ne.

’Yan sanda na buƙatar a tunatar da su cewa Nijeriya ƙasa ce mai tsarin dimokuraɗiyya, wacce ke kiyaye haƙƙin ‘yan ƙasa ba tare da take shi ba. Babu wani dalili da zai sa su nemi izini daga kotu domin hana jam’iyyun siyasa gudanar da taro.

Rundunar da ke fama da matsaloli da dama — ƙarancin kuɗi, rashin kayan aiki, cin hanci da taɓarɓarewar suna — ba za ta ƙara wa kanta cikas ba ta hanyar kawo cikas ga tafiyar dimokuraɗiyya.

A ganinmu, wannan abin da ‘yan sanda suka aikata barazana ce ga ƙasar da ke son ci gaba. A saboda haka, muna yaba wa kotun Kaduna bisa wannan hukunci mai ƙarfi da ya zama abin koyi ga sauran.

Hukuncin Mai Shari’a Zubairu nasara ce ba wai ga jam’iyyun ADC da SDP kaɗai ba, har ma ga kowane ɗan Nijeriya — domin ya sake tabbatar da cewa akwai haƙƙoƙin da babu mai isa ya karɓe su.

A matsayinmu na jarida, muna ganin hukuncin tara na naira miliyan 15 da aka ɗora wa ‘yan sanda ya yi kaɗan. Ya kamata ya fi haka domin zama darasi ga masu son take haƙƙin jama’a a gaba.

Ko da yake akwai yiwuwar rundunar ta ɗaukaka ƙara, abu mafi muhimmanci shi ne a tabbatar da cewa wannan tarar an biya ta, domin tabbatar da gaskiya da adalci.

A ƙarshe, abin da wannan hukunci ya sake tabbatarwa shi ne cewa babu wata hukuma ko jami’in tsaro da zai iya hana tafiyar da siyasa a Nijeriya — domin dimokuraɗjyya ta fi ƙarfin duk wata irin tsangwama.

By ukarofi