Badaƙalar N11bn: DSS da NIS sun sa tsohon mashawarcin El-Rufa’i a sahun waɗanda suke nema

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Hukumar hana rashawa da ayyuka masu alaƙa da ita, ICPC ta gayyaci tsohon mai bai wa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i shawara, Jimi Lawal kan zargin badaƙalar kuɗin aikin wuta ta tashar jirgin ƙasa wanda adadinsu ya kai Naira biliyan 11.

An gano cewa babu wata takardar kwantiragin aikin amma ana zargin an ware tsabar kuɗin domin gudanar da shi.

A jiya ne aka tsammaci Lawal ya gurfana a gaban jami’an ICPC domin gudanar da bincike akan sa, amma bai samu halarta ba.

ICPC ta buƙaci hukumomin ƴan sandan farin kaya (DSS) da na shige-da-fice (NIS) su sanya shi acikin jadawalin waɗanda ake nema a filayen jiragen sama, tashar jirgin ruwa da kuma kan iyakoki domin cafke shi.

Sannan, ICPC ta ce ta na tuhumar Lawal da hannu a cikin karɓo bashi a gida Nijeriya da ma ƙasashen waje ba tare da bin ƙa’idodin karɓowa ba.

Haka nan, hukumar ta gano cewa a bayanan asusunsa akwai rasiti na Naira miliyan 144 daga kamfanoni guda huɗu mallakar kai.

Hakan na zuwa ne sakamakon waiwayar gwamnatin El-Rufa’i da hukumar ta yi inda a watan Yuni da ya gabata ne ƙwarya-ƙwaryar kwamitin bincike da majalisar dokokin jihar ta kafa ya gano cewa akwai ƙuɗaɗen da ake zargin an sauya akalarsu a ƙarƙashin gwamnatin da adadinsu ya kai Naira biliyan 423,115,028,072.88.

By Babaji