Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Ƙasa a karon farko

Spread the love

A ranar Talata, shugaban ƙasa Bola Tinubu ya jagoranci taron majalisa ƙasa karo na farko tun hawan shi mulki a watan Mayu 2023.

Majalisar ƙasar ta ƙunshi, shugaban ƙasa, wanda shine jagora, sai mataimakin shugaban ƙasa wanda shine mataimaki, duk tsofaffin shugabannin ƙasar na baya, tsofaffin Alƙalan ƙasa, shugaban majalisar dattawa da tarayya, gwamnoni 36 da ministan Abuja da kuma ministan shari’a da lauyan gwamnatin tarayya.

Majalisar ƙasar ta na taka muhimmiyar rawa wajen ba shugaban ƙasa shawara a harkokin ƙasa da su ka shafi tsaro da tattalin arziki.

Majalisar ta na ba da shawara a kan bada kyautukan ƙasa, da hukumar ƙidaya ta ƙasa da sauran su.

Tsohon shugaban ƙasa Yakubu Gowon a shekarar 1975.

Taron na yau, zai bada himma wajen tattauna batutuwan a kan tsaro, tattalin arziki da kuma ƙarancin abinci.

By ukarofi