Dole ce ta sa ni sana’ar ɗinki don gadon ta na yi – Maryam Abubakar

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

A ci gaba da tattaunawa da mata kan sana’oin su, shafin Gimbiya na wannan mako ya ɗauko wa masu karatu wata matashiya da ke sana’ar ɗinkin yara. 

A tattaunawar mai karatu zai ji yadda ta zama tela da irin ƙalubalen da take fuskanta da kuma nasarorin da ta samu. Baya ga haka, baƙuwar tamu ta taɓo muhimmancin sana’a ga mata a irin wannan lokacin da muke ciki da kuma yadda sana’ar ‘ya mace ke da amfani. 

Hakazalika baƙuwar ta bayyana mana yadda ta samu jajirtacciyar uwa da ta tabbatar ta koyar da ‘ya’yanta irin sana’ar da take yi, wato ɗinki tun suna da ƙarancin shekaru, don tabbatar da ta bar masu abinda za su iya riƙe kansu a gaba.

Don haka idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Maryam Abubakar.

MANHAJA: Mu fara da jin ko wacce ce baƙuwar tamu?

MARYAM ABUBAKAR: Assalamu alaikum. Sunana Maryam Abubakar wadda a ka fi sani da marnoorr creatiɓe a kafafen sadarwa. Ni ‘yar asalin garin Kaduna ce. An haife ni a Kaduna, na yi makaratar firamare a Misbahus-Sunanh primary school da ke a Mutum ɗaya Karim Lamido, Jihar Taraba. Na yi makarantar sakandare a GGC Doma Jihar Gombe. Ina da aure, kuma ina zaune da mijina a Kaduna.

Me aka sa gaba ta ɓangaren dogaro da kai?

Ni tela ce kuma ‘yar kasuwa. Sana’ar ɗinki gado ce da mu ka yi wurin mahaifiyarmu. Wannan ya sa duk kusan daɗinmu mun iya ɗinki kuma mun ɗauke shi matsayin sana’a.

Baya ga wannan, wani ɓangaren Ina da ƙaramin kamfanina da nake yin ɗankunne da kayan ƙawata gida, wadda na fara sana’ar ta ɗankunne a shekarar 2023.

Shin ki zaɓi sana’ar ɗinki ne don kawai tana gado ko kuwa ke ma kina da sha’awa?

Gaskiya banda ra’ayin sana’ar ɗinki kusan dole ne ya zame min saboda ana yi a gidanmu na tashi na gani saboda ni ban ma san ya akai na iya ɗinki ba, saboda ban son yi a lokutan sallah, saboda yanda ɗinki yake mana yawa har cewa nake dama ace ban iya ba da yanzu ni ina hutawa.

Ko za ki iya sanar da mu yadda aka yi dukka ‘yan uwanki suke yin sana’ar da mahaifiyarki ke yi?

Dukkan mu mata ne kuma mu huɗu, saidai zan alaƙanta hakan da kawai haka Allah ya nufa, saboda kowaccen mu lokacin a shekara goma mun iya ɗinki musamman na yara.

Ko akwai darasin da ki ka koya kan koyar da ke sana’a da mahaifiyarki ta yi?

Darasin da na koya shi ne, babbar jari ne koyawa yara sana’ar hannu tun a ƙananun shekarun su saboda yanayi da rayuwar da muke ciki, wanda a so tari wannan sana’a ta fitar dani kunya kuma har gobe tana fitar dani kuma ina alfahari da ita. 

Yarana kuma ya danganta da ra’ayinsu, idan suna so zan koya musu insha Allah, idan suka nuna ba sa san ɗinki akwai sana’o’i n hannu da yawa da za su iya yi.

Kenan ba ki da ra’ayin koyar da naki ‘ya’yan sana’ar ɗinki kamar yadda aka yi maki?

Wannan ra’ayin ya zama nasu, idan suna da interest a ɗinki, ma sha Allah, idan kuma ɓangaren resin art za su ɗauka shi ma falillahil hamdu, sana’a ce me kyau.

A cikin kowacce sana’a akwai ƙalubale. Ko za ki iya sanar da mu irin waɗanda ki ke samu a harkar ɗinki?

Alhamdulillah ƙalubale ɗaya ne na fuskan ta a sana’ar ɗinki shi ne jari, saboda ni na bambanta ɓangaren da nake a madadin a ko yaushe mutane su za su kawo kayan su in ɗinka to ni sai na fito da wani tsarin, ina yin kayan sai su siya kuma har gobe ina yi idan mutum ya kawo kayan shi ɗin ma.

Waɗanne irin nasarori ki ka samu a sana’ar ɗinki?

Alhamdulillah nasarori da na samu game da sana’ar ɗinki ba za su ƙirgu ba, sai dai godiyar Allah.

Za mu so ki sanar da mu ire-iren ɗinkunan da ki ke yi?

Ni ɓangaren da na fi bada ƙarfi akai shi ne ɗinkin yara saboda yanda nake ƙaunar yara, so ina son duk wani abu da ya shafe su.

A wannan yanayin da muke ciki na tsadar rayuwa a wane matsayi za ki ajiye sana’ar ‘ya mace?

Sanaar ‘ya mace a wannan yanayin gaskiya yana cikin ƙalubale tashin da Naira ke yi ya sa wasu matan ma sun daina sana’ar wasu jarin kwata kwata bai fi dubu biyar ba abinda za ka siya dubu biyar yanzu ya tasanwa dubu goma, mata muna buƙatar taimako sosai a wannan yanayin gaskiya.

Wane kira za ki yi ga mata masu zaman kashe wando?

Kina mace ai zama ma bai ganki ba ya zama dole a tashi a kama sana’a, ko badan uzirin kanki ba kina da iyaye, ‘yan uwa za ki so ki yi musu alkhairi.

Ba kowane lokaci ne ake faɗawa miji matsalar da wasu suka kawo miki na yau da kullum ba, ke ma ya kamata ki yi iya ƙoƙarin ki wanda ba lallai miji ya ma san anyi ba.

Matan da mazajensu ke hana su neman na kai, wacce shawara za ki ba su?

To shawara ta gare su kar su gaji, su yi ta nuna musu amfanin hakan, wataƙila su samu nasara. Amma idan sun ƙi, sun dage, a haƙura cin ai ta mu su addu’a Allah Ya buɗa mu su, Ya ba su damar sauke nauyin su da ke kansu.

Shin za ki iya ƙyale ‘yar ki idan ta ce ba ta da sha’awar koyon sana’a ko yin ta?

Eh sosai zan ma ƙarfafa mata gwiwa in bata shawarwari, fatana dai yakasance ta kare mutuncin kanta.

Ko akwai wani abu da ya taɓa faruwa da ke kan sana’arki da ki ka ji kamar ki haƙura da ita?

Eh sosai, ya sha faruwa, wasu lokutan nakan kwance keken ma insa ta ɗaki ince na fasa yin sana’ar. musamman hauhawan farashin kayan ɗinki tunda ƙaramin jari gare ni ba siya da yawa nake na aje ba, su kuma mutanen mu ba sa gane wa, zakai ta aiki ba riba, kullum to irin wannan yakansa min wasi-wasi a raina, amma idan na yi tunani ina da ‘future’ da nake hange a gaba kuma mijina yana ƙarfafa min gwiwa sai inji idan na sare banyi mishi adalci ba wannan shike ƙara samin ƙwarin gwiwa inci gaba da sana’ata.

Ko akwai wani abu da ki ke yi na ganin mata sun amfana da sana’ar da ki ke yi ta hanyar koyar da wasu?

Ina son inga kowa yana da abinda ya dogara da shi musamman mata, shiyasa nake koyar da su ɗinki a ‘chennel’ ɗina a Telegram don dogaro da kai saboda su rage zaman banza da yawan gulmace-gulmace.

Idan mace na sha’awar yin sana’ar ɗinki me take buƙata?

Da farko tasa abin a cikin ranta ya zama abu ne da take da sha’awa saboda duk abinda ka ke da sha’awa duk wani ƙalubale da zai same ka bazaka yi ‘giɓe up’ da wuri ba.

Sai keken ɗinki da kayan aiki.

Wane matsayi za ki ɗora irin kwalliyar da mata ke yi a wannan zamani?

To kowa yana da zaɓin shi kuma kowa yana da ra’ayin shi ni dai bana ra’ayin ire-iren wannan kwalliyan.

Wacce irin kwalliya ki ka fi son yi?

Ni na fi son in shafa man baki insa kwalli sai powder shima ba ko yaushe ba sai wani sa’in nakan sa jambaki ya danganta da yanayin da nake ciki

Mun gode.

Ni ma na gode sosai.

By ukarofi