NYSC ta soke takardar shaidar kammalawa na mutum 101

Spread the love

Hukumar NYSC ta soke takardar shaidar kammalawa ga aƙalla mutum 101 bisa zargin sun shiga tsarin ta haramtacciyar hanya. Waɗanda abun ya shafa sun kasance daga jami’ar Calabar daga shekara ta 2021, 2022 da 2023.

Wannan ya fito daga bakin Eddy Megwa wanda shine jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, ya bayyana cewa wannan matakin ya biyo bayan wani bincike da aka yi wanda ya janyo soke shaidar kammalawar ga mutanen.

Ya bayyana cewa mutane su lura da waɗanda ke ikirarin sun kammala horon saboda yanzu hukumar ta fitar da sabbin hanyoyi tantance takardar shaidar kammalawa.

Daga ƙarshe ya bayyana, ɗalibai da su ka gama karatu a makarantun ƙasashen waje za a cigaba da tantance su domin a tabbatar da sahihanchin makarantun.

By ukarofi