Nijeriya za ta fara ƙera kayayyakin soja – Matawalle

Spread the love

Nijeriya na daf da fara ƙera kayayyakin soja da kanta nan bada jimawa ba. Wannan ya fito bakin ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle a wani taron manema labarai na taron bikin cika shekara 60 na kamfanin tsaro na Nijeriya(DICON)

Ya bayyana irin rawar da kamfanin ke takawa a harkokin tsaron Nijeriya domin inganta shi.

Babban abin farin ciki shine, a taron za a gudanar da wani taro na farko na kamfanin tsaron Afirka a ɗakin taro na Shehu Musa Yar’adua.

Ya ƙara da cewa, sanya hannu ga sabuwar dokar kamfanin tsaron na 2023 wanda shugaban ƙasa Bola Tinubu yayi zai ba mutane ƙwarin gwiwa su shiga cikin kamfanin domin bada gudunmuwar su.

Matawalle yayi kira ga masu ruwa da tsaki ‘yan kasuwa su shigo kamfanin domin ganin an samu cigaba mai ɗorewa a harkar tsaro.

By ukarofi