Hukumar gudanar da jarrabawar WAEC ta fitar da sakamakon jarabawar WAEC na ɗaliban sakandire na shekarar 2024.
Hukumar ta bayyana hakan a wani saƙon da ta wallafa a ranar Litinin kan shafinta na X.
A cikin saƙon ta na cewa, “Hukumar gudanar da jarabawar WAEC tana farin ciki da sanar da waɗanda suka rubuta jarrabawar WAEC na shekarar 2024 cewa an saki sakamakon a hukumance a yau Litinin, 12 ga Agusta, 2024.”
Ɗaliban da suka rubuta jarrabawar WAEC a shekarar 2024 za su iya duba sakamakonsu ta hanyoyi daban-daban da WAEC ta samar.
Domin tabbatar da sauƙin samun sakamakon, WAEC ta sauƙaƙe hanyar duba sakamakon ga dukkan ɗalibai.
Yadda za ka duba sakamakon WAEC Na 2024:
- Duba Sakamakon WAEC Ta intanet (Online):
- Ziyarci shafin duba sakamakon na hukumar WAEC: (https://waecdirect.org)
- Saka lambar jarabawar WAEC mai lambobi 10 a cikin filin da aka tanadar.
- Saka lambobi 4 na Shekarar jarrabawar, misali 2024
- Zaɓi irin jarrabawar
- Saka lambar shaidar e-PIN Voucher
- Saka lambar sirri (PIN), e-PIN ɗinka
- Danna aika, sai ka jira sakamakon ya bayyana.
- Ta SMS:
- Buɗe manhajar aika saƙonnin tes (SMS) ɗinka.
- Aika saƙon tes a tsari kamar haka: WAECExamNoPINExamYear zuwa lambar 32327 (Ga masu amfani da layin MTN, Airtel, da Glo).
- Misali: WAEC1234567890123456782024.
- Sakamakon jarrabawar a wayarka zai bayyana
- Bi umarnin da ke cikin manhajar don samun damar ganin sakamakonka.
Lura: MTN, Glo, da Airtel ne masu amfani da layin za su iya duba sakamakon WAEC ɗinsu ta amfani da wannan hanyar ta SMS.
Ana cajin kuɗin aika saƙon tes lokacin duba sakamakon WAEC ɗinku ta amfani da saƙonnin tes.
- Manhajar Wayar WAEC:
- Sauke manhajar WAEC daga Google Play Store ko Apple App Store.
- Bi umarnin da ke cikin manhajar don samun damar duba sakamakonka.
