Kwamitin bincike ya miƙa aikin sa ga Shugaban Ƙaramar hukumar Ungoggo

Spread the love

Daga RABI’U SANUSI

Shugaban Kwamitin Kula da binciken kadarori da aka kafa a Ƙaramar hukumar Ungogo, Dr. Saminu Umar Rijiyar Zaki, ya kammala aikinsa ya kuma gabatar da rahoton ga shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Ungoggo Alh sani Abdu Ungoggo a ofishinsa.

Wannan na zuwa ne a wata sanarwa da mai magana da yawun ƙaramar hukumar ta Ungoggo Malam Adamu ya fitar ga manema labarai

Rahoton, wanda ya ƙunshi ayyuka, ci gaba, da ƙalubalen da ƙaramar hukumar ta fuskanta yayin lokacin canjin shugabanci,

Dr. Saminu Umar ya nuna godiya bisa damar da aka ba shi na jagoranci tare da jaddada manyan ɓangarorin da za a mayar da hankali kansu a lokacin shugabancinsa, ciki har da ci gaban ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, da haɗin kai da al’umma.

Jami’in riƙon na ƙaramar hukumar Ungoggo Alh sani Abdu bayan karɓar rahoton, ya yabawa Dr. Saminu Umar da dukkan kwamitin kula da canji bisa ƙwazo da jajircewar su.

Ya kuma ƙara da cewa za a binciki aiyyukan kwamitin da yakawo tare da shawarwari da suka bayar.

By ukarofi