Mutuwar waɗanda ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a hannun jami’an tsaro a Minna, Jihar Neja, da kuma sabon ruftawar ramin haƙar ma’adinai a Jihar Taraba, sun sake tunatar da Nijeriya irin munin matsalar haƙar ma’adinai da har yanzu ba a samu mafita gare ta ba.
A Minna, mutane 33 sun mutu yayin da suke hannun jami’an tsaro, yayin da a Taraba ƙasa ta rufta a kan wasu masu haƙar ma’adinai 20 a ƙarƙashin wani rami mai hatsari. Waɗannan masifu guda biyu na buƙatar a gano gaskiyar abin da ya faru tare da ɗaukar alhakin laifin da aka aikata.
Mutuwar mutanen Minna ta fi tayar da hankali saboda har yanzu akwai saɓanin bayanai kan yadda abin ya faru. Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Nijeriya (NSCDC) da wasu jami’an gwamnati sun danganta mutuwar da rashin lafiya da kuma yiwuwar ɓarkewar wata cuta. Sai dai waɗanda suka tsira da rayukansu da shaidu sun yi zargin cewa cunkoso, rashin isasshen iska da kuma wasu munanan yanayi a wurin da ake tsare da mutanen ne suka haddasa matsalar. Bincike mai zaman kansa, sahihi kuma bayyananne ne kaɗai zai iya warware wannan saɓanin bayanai.
Shugaba Bola Tinubu ya nuna fushinsa kan lamarin tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike, yayin da Gwamnatin Jihar Neja ta amince da faruwar mutuwar tare da fara ƙoƙarin gano ainihin abin da ya faru. Ya kamata jama’a su yi haƙuri su bari bincike ya gano gaskiya. Amma bai kamata a yi ƙoƙarin ɓoye abin da ya faru ba. Duk wanda aka samu da hannu bisa ingantattun hujjoji, dole ne a gurfanar da shi a gaban shari’a, ba tare da la’akari da matsayinsa ko kujerarsa ba.
A wannan batu, sahihancin binciken yana da matuƙar muhimmanci. Binciken da hukumomin da ake zargi da hannu wajen gudanar da lamarin za su gudanar shi kaɗai zai yi wahala ya samu cikakken amincewar jama’a. Ya kamata a kafa kwamitin shari’a ko kuma a bai wa Hukumar Kare Haƙƙin Bil’adama ta ƙasa (NHRC), tare da haɗin gwiwar ƙwararrun likitoci masu zaman kansu, damar gano musabbabin kowace mutuwa. Haka kuma, ya kamata a wallafa sakamakon binciken cikin wani ƙayyadadden lokaci.
Lamarin na Minna ya kuma shiga cikin jerin abubuwan da ke nuna wani yanayi mai tayar da hankali na asarar rayukan fararen hula sakamakon wasu ayyukan hukumomin gwamnati a Arewacin Nijeriya, ciki har da hare-haren sama na sojoji da suka taɓa hallaka fararen hula marasa laifi. Ko wurin da ake tsare da mutane ne ko kuma aikin soji, ƙa’idar ba ta canja ba: dole ne hukumomin tsaro su gudanar da ayyukansu cikin ƙwarewa, sannan su ɗauki alhakin kare rayukan mutanen da ke ƙarƙashin kulawarsu.
Rushewar ramin haƙar ma’adinai a Mayo Kam, da ke ƙaramar Hukumar Bali a Jihar Taraba, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, ya sake fallasa haɗarin haƙar ma’adinai ba tare da cikakken tsari ba da kuma rashin ingantattun matakan kare lafiyar masu aikin.
Wannan lamari ya kuma tuna da irin abubuwan da suka faru a baya. A watan Nuwamban 2024, yankin Gashaka-Gumti da ya ratsa sassan jihohin Taraba da Adamawa ya fuskanci rushewar wani ramin haƙar ma’adinai mai muni, inda aka yi fargabar cewa kusan masu haƙar ma’adinai 22 sun maƙale ko sun mutu. Ci gaba da faruwar irin waɗannan bala’o’i na nuna cewa darussan da aka koya daga abubuwan da suka gabata ba su haifar da ingantattun matakan kariya ba. Wannan ba abu ne da ya kamata ya ci gaba ba.
Nijeriya na buƙatar cikakkiyar manufar harkar ma’adinai wadda za ta magance haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, tare da samar da ingantaccen tsari mai aminci ga masu haƙar ma’adinai na gargajiya da ƙanana da ke gudanar da ayyukansu bisa ƙa’ida.
Wannan na buƙatar sauƙaƙa tsarin bayar da lasisi, ta yadda ƙananan masu haƙar ma’adinai za su samu ƙwarin gwiwar yin aiki bisa doka. Haka kuma, dole ne a samar da ƙa’idojin kare lafiyar ma’aikata da ba za a yi wasa da su ba, tare da horar da jami’an binciken wuraren haƙar ma’adinai da kuma tabbatar da cewa suna ziyartar wuraren aikin akai-akai.
Bayar da lasisi, duba wuraren haƙar ma’adinai, kare muhalli da kuma aiwatar da ƙa’idojin tsaro dole ne su kasance cikin tsari mai inganci, ba tare da nuna bambanci ko fifita wani ba.
Haka kuma, ana ci gaba da samun zarge-zargen cewa wasu manyan mutane da jami’an gwamnati kan haɗa kai da wasu marasa kishin ƙasa wajen gudanar da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba. Bai kamata a ɗauki waɗannan zarge-zarge a matsayin gaskiya ba tare da hujja ba, kamar yadda bai kamata a yi watsi da su kai tsaye ba. Inda aka samu sahihan hujjoji, dole ne a gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.
Ya kamata a gudanar da cikakken bincike kan mutuwar mutanen Minna da kuma waɗanda suka rasa rayukansu a Taraba, da manufa guda mai sauƙi: gano gaskiya, hukunta duk wanda aka samu da laifi da kuma daukar matakan da za su hana sake faruwar irin waɗannan masifu.
Albarkatun ma’adinan Nijeriya ya kamata su zama ginshiƙin bunƙasar ƙasa da ci gabanta, ba sanadin mutuwar mutane da za a iya kauce wa ba.
Haƙar ma’adinai ba za ta taɓa zama lasisin kashe mutane ba.
