Bai kamata mu sauya al’adunmu don fim ɗinmu ya samu karɓuwa a duniya ba – Mo Abudu 

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Mai karatu, barkanmu da sake kasancewa da ku a shafin Taurari na jaridarku ta Blueprint Manhaja, shafin da ke kawo muku labaran fitattun jarumai da abubuwan da suka shafi harkar nishaɗantarwa, tare da waiwayar rayuwarsu da abubuwan da suka taimaka wajen kai su inda suke a yau.

A duk lokacin da ake magana kan ci gaban masana’antar fina-finai ta Najeriya, ba za a iya kaucewa ambaton mutanen da suka taka muhimmiyar rawa wajen samar da fina-finan da suka sauya yadda ake kallon Nollywood ba. Wasu sun yi fice ta hanyar bajintar da suke nunawa a gaban kyamara, wasu sun shahara wajen bayar da umarni, yayin da wasu suka zaɓi zama a bayan fage, inda suke amfani da tunaninsu, jarinsu da ƙwarewarsu wajen samar da fina-finan da za su iya kai labaran al’ummarsu zuwa ga masu kallo a sassan duniya.

ɗaya daga cikin matan da suka yi fice a wannan fanni ita ce Mosunmola Abudu, wadda aka fi sani da Mo Abudu. Sunanta ya zama ɗaya daga cikin muhimman sunayen da ake ambato idan ana magana kan samar da manyan fina-finan Nollywood, musamman waɗanda suka samu damar fita daga kasuwar Najeriya zuwa manyan kafafen fina-finai na duniya.

Sai dai abin da ya fi ban sha’awa a tarihin Mo ba wai yawan fina-finan da ta samar ko yarjejeniyoyin da ta kulla da manyan kamfanonin duniya ba ne. Abin da ya fi jan hankali shi ne hangen nesan da ta shigo da shi masana’antar, na ganin cewa Afirka tana da labaran da suka cancanci a ji, kuma bai kamata a bar wasu mutane daga wajen nahiyar su zama su kadai ke ba da labarin rayuwar ‘yan Afirka ba.

Wannan buri ne ya zama ginshikin tafiyarta, tun daga kafuwar EbonyLife har zuwa samar da fina-finan da suka samu karɓuwa a gidajen sinima da kafafen yaɗa fina-finai na duniya. Amma kafin ta kai wannan matsayi, akwai tafiyar rayuwa mai cike da sauye-sauye, jajircewa da kuma yanke shawarar shiga wani fanni da ba shi ne ta fara karantawa ko aiki a cikinsa ba.

Shin wace ce Mo Abudu?

An haifi Mosunmola Abudu a ranar 11 ga watan Satumban 1964 a Hammersmith, da ke birnin Landan na ƙasar Ingila, amma iyayenta ‘yan asalin garin Ondo ne da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Ta shafe wani ɓangare na yarintarta a Ingila, amma tana da shekara bakwai iyayenta suka mayar da ita Najeriya domin zama tare da kakanninta. Daga baya, tana da shekara 11, ta koma Ingila domin ci gaba da karatunta.

Ta yi karatun digiri na biyu a fannin kula da ma’aikata a Jami’ar Westminster da ke Landan, sannan ta fara aikin kula da ma’aikata a shekarar 1987. A shekarar 1993 ta koma Najeriya, inda ta ci gaba da aikinta a kamfanin EɗɗonMobil.

Daga baya ta kafa kamfanin tuntuba kan harkokin ma’aikata mai suna Vic Lawrence & Associates a shekarar 2000.

Waɗannan bayanai suna da muhimmanci wajen fahimtar yadda ta shigo harkar fina-finai, domin Mo ba ta taso a matsayin jaruma ko mai shirya fina-finai ba. Ba kuma a wannan fanni ta fara samun kuɗin shiga ba. Ta shafe shekaru tana aiki a wani ɓangare daban kafin ta yanke shawarar bin wata hanya da ta fi dacewa da burinta na kawo sauyi a kafafen yaɗa labarai.

A shekarar 2006, Mo ta fara gabatar da wani shirin talabijin mai suna Moments with Mo, wanda ya kasance ɗaya daga cikin muhimman matakan farko na shigarta kafafen yaɗa labarai.

Shirin ya ba ta damar tattaunawa da fitattun mutane daga ɓangarori daban-daban na rayuwa, ciki har da siyasa, kasuwanci, nishaɗi da zamantakewa. Ta hanyar hirarrakin da take yi, ta samu damar sanin irin batutuwan da suka shafi al’umma da kuma yadda za a iya amfani da kafafen yaɗa labarai wajen kawo su ga jama’a.

Sai dai yayin da take gudanar da wannan aiki, ta fara fahimtar cewa tana son yin fiye da gabatar da shirye-shirye. Tana son samun kafar da za ta iya amfani da ita wajen samar da labaran Afirka da kuma nuna al’adu, dabi’u da irin rayuwar da ake yi a nahiyar.

Wannan tunani ya kai ta ga kafa EbonyLife TV a shekarar 2013, wata kafar talabijin da ta mayar da hankali kan shirye-shiryen nishaɗi da labaran Afirka.

A shekarar 2014 kuwa, ta kafa EbonyLife Films, kamfanin da daga baya ya zama babban ginshikin ayyukanta na shirya fina-finai.

A wannan lokaci ne burinta ya fara ɗaukar sabon salo. Maimakon ta tsaya kan samar da shirye-shiryen talabijin, ta fara shiga wani ɓangare na masana’antar da ke bukatar hada fasaha, tunanin ƙirƙira, jarin gudanarwa da kuma fahimtar kasuwar fina-finai.

Me ya sa ta zaɓi harkar fina-finai?

A wata hira da jaridar The Guardian ta yi da ita a shekarar 2024, Mo ta yi bayani kan ɗaya daga cikin abubuwan da suka motsa ta wajen shiga harkar yaɗa labarai da shirya fina-finai.

Ta ce ta fahimci cewa ba a bayar da labaran Afirka da al’ummarta yadda suka cancanta ba, kuma wannan fahimta ce ta sanya ta ƙuduri aniyar samar da wata kafa da za ta ba da damar nuna waɗannan labarai.

“Na yi imani da ƙarfin labaran Afirka, kuma na san duniya a shirye take ta saurare su,” inji ta.

Wannan magana tana bayyana falsafar da ta gina a kanta tun farkon shigarta masana’antar.

A ganinta, ba lallai ne labaran Afirka su zama waɗanda suka shafi talauci, yaƙi, yunwa da sauran matsaloli kawai ba. Nahiyar tana da labaran soyayya, kasuwanci, kimiyya, al’adu, tarihi, nasara da kuma rayuwar yau da kullum waɗanda suka cancanci samun gurbi a fina-finan duniya.

Sai dai ta fahimci cewa samun damar isar da waɗannan labarai yana bukatar kafa kamfani da zai iya samar da fina-finai masu inganci, tare da samun hanyar da za su isa ga masu kallo a kasuwanni daban-daban.

A hirar da ta yi da The Guardian, ta kuma bayyana cewa tana fuskantar rashin yarda daga wasu mutane game da yiwuwar samun kasuwar fina-finan Afirka a duniya. Wasu na da shakku kan ko masu kallo a kasashen waje za su iya karɓar irin waɗannan labarai.

Amma ta ce ta dage kan abin da ta yi imani da shi, tare da hada kai da mutanen da suke da irin wannan hangen nesa. 

Bayan kafa EbonyLife Films, ɗaya daga cikin manyan ayyukan farko da suka fito daga kamfanin shi ne fim ɗin ‘Fifty’, wanda aka fitar a shekarar 2015.

Fim ɗin ya ba da labarin rayuwar wasu mata huɗu da suka kai shekaru 50, inda kowannensu ke ƙoƙarin fuskantar ƙalubalen da suka shafi soyayya, aure, iyali, sana’a da kuma neman farin cikin rayuwa.

Aikin ya samu karɓuwa a Najeriya, inda ya zama ɗaya daga cikin fina-finan da suka nuna irin damar da ke cikin samar da labaran mata masu shekaru, waɗanda ba kasafai ake mayar da rayuwarsu babban jigon fina-finan kasuwanci ba.

Mo ta kasance babbar mai samar da fim ɗin, yayin da Biyi Bandele ya jagoranci bayar da umarninsa.

Abin lura a nan shi ne, tun a wannan aikin, an fara ganin irin salon da EbonyLife ke son bi wajen samar da fina-finai, wato haɗa labaran da suka shafi rayuwar al’umma da nishaɗi, tare da amfani da fitattun jarumai da ingantaccen tsarin samar da fim.

Idan akwai wani fim da ya taimaka matuƙa wajen ƙara fito da sunan Mo Abudu a harkar shirya fina-finai, to kuwa ‘The Wedding Party’ na shekarar 2016 yana daga cikin manyan ayyukan da za a ambata.

Fim ɗin ya mayar da hankali kan bikin auren wasu masoya, inda shirye-shiryen da suka shafi iyalai biyu suka haifar da barkwanci, saɓani da abubuwan da suka sa labarin ya kayatar.

An haɗa fitattun jaruman Nollywood a cikin fim ɗin, ciki har da Adesua Etomi, Banky W, Richard Mofe-Damijo, Sola Sobowale da Ireti Doyle.

Kemi Adetiba ce ta bayar da umarni, yayin da Mo Abudu ta kasance cikin manyan masu samar da aikin ƙarƙashin ƙungiyar ELFIKE Collective, wadda ta haɗa EbonyLife Films, FilmOne Entertainment, Inkblot Productions da Koga Studios.

Fim ɗin ya samu gagarumar karɓuwa a gidajen sinima, inda ya samu sama da naira miliyan 450 a lokacin da aka haɗa kuɗaɗen shigarsa. A lokacin, ya zama fim ɗin Najeriya mafi yawan kuɗaɗen shiga a tarihin gidajen sinima.

A wani bayani da Mo ta yi bayan nasarar fim ɗin, ta ce burinsu tun farko shi ne samar da fim mai inganci wanda duk wani ɗan Najeriya zai yi alfahari da shi, kuma zai iya danganta kansa da labarinsa.

Ta kuma bayyana cewa nasarar fim ɗin ta nuna cewa fina-finan Nollywood masu inganci za su iya yin gogayya da manyan fina-finan Hollywood a kasuwarsu ta gida.

Wannan nasara ta kasance muhimmin mataki ba kawai ga Mo ba, har ma ga masana’antar fina-finan Najeriya, domin ta ƙara tabbatar da cewa masu shirya fina-finai za su iya samun gagarumar kasuwa idan suka samar da ayyukan da suka dace da buƙatun masu kallo. 

Ba a tsaya nan ba, domin a shekarar 2017 aka fitar da kashi na biyu na fim din mai suna ‘The Wedding Party 2: Destination Dubai’. A wannan karon, an fadada labarin zuwa birnin Dubai, inda aka sake haɗa wasu daga cikin jaruman da suka taka rawa a kashi na farko.

Fim ɗin ma ya samu karɓuwa a gidajen sinima, inda ya ƙara tabbatar da cewa nasarar kashi na farko ba ta kasance ta bazata ba.

Bayan nasarar ‘The Wedding Party’, Mo da kamfaninta sun ci gaba da samar da wasu fina-finai da suka samu karɓuwa.

Daga cikinsu akwai ‘The Royal Hibiscus Hotel’ na shekarar 2017, wanda ya yi magana kan soyayya, iyali da kasuwancin otal; ‘Chief Daddy’ na 2018, wanda ya mayar da hankali kan rikicin da ya kunno kai tsakanin iyalan wani attajiri bayan rasuwarsa; da kuma ‘Your Eɗcellency’ na 2019, wanda ya yi amfani da barkwanci wajen nuna tasirin kafafen sada zumunta a harkokin siyasa.

A cikin waɗannan ayyuka, Mo ta ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan mutanen da ke kula da samar da fina-finai, tare da hada kai da daraktoci, marubuta da sauran kwararru domin ganin an kai ayyukan ga masu kallo.

Ba wai kawai ta tsaya kan irin labaran da suka shafi soyayya da barkwanci ba, ta kuma fara amfani da fina-finai wajen jawo hankalin al’umma kan matsalolin da suka shafi rayuwar jama’a.

A shekarar 2020, EbonyLife ya fitar da fim ɗin ‘Òlòtūré’, wanda ya bambanta da wasu daga cikin fina-finan da kamfanin ya saba samarwa.

Fim ɗin ya yi magana kan fataucin mutane, musamman yadda wasu mata ke faɗawa hannun masu safarar mutane bisa alƙawarin samun damar rayuwa mafi kyau a ƙasashen waje.

Labarin ya bi wata ‘yar jarida da ta shiga cikin wannan harkar a ɓoye domin gano yadda ake gudanar da ita da kuma irin cin zarafin da mata ke fuskanta.

A wannan aiki, Mo Abudu ta kasance babbar mai samar da fim ɗin (Eɗecutive Producer), yayin da Kenneth Gyang ya bayar da umarni.

Netfliɗ ya ɗauki fim ɗin a matsayin ɗaya daga cikin ayyukansa na musamman daga Najeriya, inda aka fara nuna shi a watan Oktoban 2020.

A wata hira da ta yi da jaridar Screen Daily a watan Disamban shekarar, Mo ta bayyana cewa labarin yana da matuƙar muhimmanci, domin a matsayinta na mai samar da fina-finai ba za ta guji batutuwan da ya kamata al’umma ta tattauna a kansu ba.

Ta kuma bayyana cewa karɓuwar fim ɗin ta ba ta mamaki, domin an samu martani daga masu kallo a ƙasashe daban-daban, ciki har da Rasha, Brazil, Japan, Sri Lanka da Indiya. Ta ce a lokacin fim ɗin ya shiga jerin fina-finai da aka fi kallo a Netfliɗ a ƙasashe 26.

By ukarofi

Leave a Reply