Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa, ƙaddamar da sayar da man fetur a farashin Naira zai taimaka wajen saita ɓangaren man da farfaɗo da darajar Naira, don haka bai dace Nijeriya ta watsa wa Shugaban Matatar Man ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangode, ƙasa a ido ba.
Mashawarci na musamman ga shugaban ƙasa kan yaɗa labarai da tsare-tsaren sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata.
Shugaba Tinubu ya kuma jinjina wa kwamitin ƙaddamar cinikin ɗanye da tataccen man a farashin Naira tare da horansu da su kawo ƙarshen matsalar da ake fama da ita.
A yayin da yake magana a Abuja a ranar Talata, shugaba Tinubu ya ce an ɓullo da amfani da Naira wajen cinikin man ne domin magance matsalar musayar kuɗin waje da ake fuskanta, domin ba zai bari ƙasar nan ta ƙara shiga halin da ta samu kanta ba cikin shekaru 40 da suka wuce.
Daga nan ya hori kamfanin NNPC da matatar ɗangote kan jajircewa wajen bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar nan da rayuwar ‘yan Nijeriya.
Sannan Shugaba Tinubu ya shawarci masu ruwa da tsaki da su mayar da hankali wajen samar da mai a cikin gida a maimakon ƙoƙarin shigo da man daga ƙetare domin ba wa mahukunta damar amfani da rarar kuɗin musayar kuɗin ƙetaren wajen bunƙasa ɓangren man.
Sannan ya umarci masu ruwa da tsaki kan su tuntuɓi Afreɗimbank domin samun shawarwari na warware batun fidda farashin ɗanye da kuma tataccen man.
“Bai kamata mu zuba wa Alhaji Aliko Ɗangote ƙasa a ido ba a ƙoƙarin mu na samar da wadataccen makamashi. Dagoro da shi zai fi zamar mana alkhairi…” a cewar shugaba Tinubu.
Shi ma da yake jawabi, ministan kuɗi da kula da tatalin arziƙin ƙasa, Wale Edun, ya ce gwamnatin ba za ta koma da baya ba kan matakin da ta ɗauka na sayar da ɗanyen mai a farashin Naira kuma ba za ta tsoma baki ba game da yadda musayar za ta zama a ɓangren man fetur.
A wurin taron, shugaban tattara haraji na ƙasa, Zach Adedeji, wanda shi ne shugaban kwamitin ayyuka na musamman, ya ce, ya kamata a kawo ƙarshen shigo da tataccen man fetur da zarar za a iya samar da wadataccen mai a cikin gida. Ya ce manufar shugaban ƙasa ita ce mayar da Najeriya ta zama ƙasa mai wadatar tataccen mai da kuma fitar da shi ƙasashen waje.
Taron ya samu halartar shugabannin daga ɓangarori da dama kamar shugaban bankin AfreɗimBank Benedict Oramah, da ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare, Abubakar Bagudu da sauran masu ruwa da tsaki a harkar man fetur.
A watan Yuli ne dai majalisar zartarwa ta fadar shugaban ƙasa, (FEC) ta umarci kamfanin man fetur na ƙasa da ya haɗa kai da matatar ɗangote da sauran ‘yan kasuwa domin warware dambarwar sayar da mai a farashin Naira.
Wannan kuwa ya biyo bayan sanar da fara sayar da man fetur a farashin Naira da gwmantin tarayya ta yi a ranar 1 ga watan Oktobar 2024.
